Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin jagorancin, Gwamna Bello Matawallen Maradun ta sake kafa dokar hana hawa Mashin a wasu unguwanni da garuruwa da ke fadin Jihar.
Bello Matawalle ya bayyana hakan ne a jiya lokacin da ya ke zantawa ga manema labarai a fadar Gwamnatin jihar bayan kammala taro da masu ruwa da tsaki a Jihar.
Ya kara da cewa duba da yadda ‘yan bindiga suka mamaye wasu yankuna da ke wajen garin Gusau, babban birnin jihar, za a dauki mataki na hana hawan babura daga karfe 8 na dare zuwa karfe 6 na safe a dukkan yankunan wajen garin Gusau.
Cikin wuraren da aka lissafa akwai kamar irinsu Mareri da Damba da Tsunami da Tsauni da kuma Barakallahu da Samaru sai Gada Biyu da Janyau ta Gabas.
Gwamnati ta umarci jami’an tsaro da su bindige duk wanda yake hawa babur tsakanin karfe 8 na dare zuwa 6 na safe a wajen Gusau idan ya ki tsayawa lokacin da suka umarce shi da ya tsaya.
Ya ce daga yanzu duk wani bako da ya nemi masauki a kowane otal dole ne ya samar da ingantaccen katin shaida.
Bello Matawalle ya ce “Ina kira ga daukacin al’ummar jihar nan da su ci gaba da taimaka wa jami’an tsaron mu da addu’a da fatan alheri wajan yaki da ‘yan fashi” in ji shi
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp