Babban Sufeton ‘yansandan Nijeriya, IGP Usman Alkali ya kaddamar da horas da jami’an ‘yansanda, da wani taron bitar hadin gwiwar jam’an tsaro da ya kunshi samar da tsaro a lokutan manyan zabukan 2023.
Kamar yadda ajandar taron ta nuna, wannan wani bangare ne na shirye-shiryen da take aiwatar wa wajen tabbatar da ganin zabukan sun gunada cikin tsanaki, ba tare da samun wata tangarda ba a babban zabe mai zuwa.
A makonnin da suka gabata ne Sufeto Janar na ‘yansandan ya gudanar da wani taron karawa juna sani na kasa baki daya a Abuja, wanda ya ayyana cewa, “ Wannan horo ne a kokarin da muke yi na musamman wanda zai kara wa kwarin gwiwa ga jami’an yan-sanda wajen ganin sun sun gudanar da ayyukan su na tsaro a lokutan zabe don a samu sahihin zabe mai cike da kwanciyar hankali.”
Taron na yini daya ranar Litinin a masaukin baki na Pinnacle Hotel dake Maiduguri tare da hadin gwiwar kamfanin tsaro na Solar Security and Consult Company. Taron mai taken: “Zaben 2023 da inganta tsaro ga kasa don samar da ingantaccen tsarin zabe a Nijeriya, da tabbatar da tsaro da oda.” Wanda kimanin wakilai a shiyoyi shida a fadin kasar nan.
A jawabin tsohon Sifeto Janar na Yan-sandan Nijeriya, kuma jami’in da yake kula da bayar da horon, ga jami’an yan sandan jihar Borno, mahalarta taron wadanda suka hada da jami’an Hukumar NDLEA, kungiyar lauyoyin Nijeriya ta NBA, kungiyoyin farar hula, yan jaridu da sauran su jama’a, Mista Solomon Arase inda ya bukaci su rinka tausasa zukata tare da bai wa kowa dama da yanci a mu’amalar yau da kullum da juna a lokacin musayar ra’ayi, a madadin Sifeto Janar na ‘Yansandan Nijeriya.