Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Southampton ba za ta buga gasar Firimiya Lig na badi ba, bayan da su ka koma gasar yan dagaji ta kasar Ingila, Southampton ta yi rashin nasara a hannun Tottenham Hotspur wanda kuma shi ne ya yi sanadiyar da Southampton ta koma gasar Championship ta kasar Ingila.
Hakan ya sa ta kasance kungiya ta farko a tarihin gasar da ta koma baya (relegation) bayan buga wasanni 31 kacal, Southampton ta samu maki 10 a wasanni 31 an zura mata kwallaye 74 a raga sannan kuma ta zura kwallaye 23 kacal a bana.
- Kano Pillars Ta Koma Ta 4 A Teburin Firimiyar Nijeriya
- Manchester United Na Son Lashe Firimiya A Shekarar 2028
Ramsdale tsohon mai tsaron ragar Arsenal, ya taka rawar gani a wasan inda ya tare kwallayen da ka iya shiga raga har sau biyar a wasan, ciki har da kwallayen da Spence da Dominic Solanke su ka buga cikin kwarewa da zafin nama, amma kuma bakin sun rasa damarsu a lokacin da Tel ya ci wani bugun daga kai sai mai tsaron raga, biyo bayan keta da Welington ya yi a kan Johnson.
Bayar da damarmakin da Southampton ta yi wani abu ne da ya ci mata tuwo a kwarya, hakan ya sa ta zama kulob din da aka fi zurawa kwallo a raga inda aka zura mata kwallo 74 a wasanni 31 da su ka buga, kuma abu ne da za su magance idan har su na son dawowa gasar Firimiya a kakar wasa mai zuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp