A ƙauyen Maikuma, da ke cikin ƙaramar hukumar Dandume ta Jihar Katsina, ana zargin wasu ƴan bindiga sun kashe mutane 4 sannan suka sace a ƙalla 45. Harin ya faru ne a daren Lahadi, lokacin da wata babbar tawagar ‘yan fashin ɗauke da makamai ta kai farmaki a cikin al’umma.
Shaidu sun bayyana cewa masu farmakin sun shige gidaje daga a jere a jere suna aiki har tsawon awanni kafin su gudu zuwa dajin da ke kusa da su tare da waɗanda suka sace.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 10, Sun Ceto Mutane 101 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina Da Zamfara.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Kwamandan ‘Yan Sa-kai, Sun Jikkata Wasu A Katsina
Duk da ƙoƙarin jami’an tsaro, ba su samu nasarar bin ƴan bindigar ba zuwa bayan iyakar garin. Shugaban ƙaramar hukumar Dandume, Basiru Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa adadin masu farmakin sun kai fiye da 100.
Musa ya nuna damuwa game da yadda hare-haren ke faruwa akai-akai, yana kira ga hukumomi su ƙara tsaurara matakan tsaro don kare al’ummomin da ke cikin hatsari. Hukumomin tsaro na Jihar Katsina har kawo yanzu ba su fitar da wata sanarwa ta hukuma ba game da lamarin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp