Dakarun sojin rundunar ‘Forest Sanity’ sun sake kashe gungun ‘yan ta’adda a wani artabu da suka yi a dajin Galbi da ke a karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.
Wannan nasarar na zuwa ne bayan kwanaki da dakarun suka hallaka ‘yan ta’adda da dama a yankin na Chikun.
- Tattalin Arzikin Sin Yana Ci Gaba Da Bunkasa Yadda Ya Kamata
- Da Dumi-Dumi: Sha’aban Sharada ya fice daga APC zuwa jam’iyyar ADP
Wata kungiyar tsaro mai zaman kanta da ake kira da Eons a sanarwar da ta wallafa a shafinta na Tiwita a yau Talata ta ce, ‘yan ta’addar sun dawo yankin da lamarin ya auku ne domin kwashe wasu daga cikin ‘yan uwansu ‘yan ta’addar da dakarun soji suka kashe a artabun da aka yi da su har aka kashe su a ranar Asabar da ta wuce.
LEADERSHIP ta ruwaito gwamnatin jihar Kaduna ta ce, a kwanakin da suka wuce dakarun na ‘Forest Sanity’ sun kashe ‘yan ta’adda da kuma ‘yan bindiga a wani luguden wuta ta sama da suka kai.
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ne, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar, inda ya ce, an kashe ‘yan ta’addar ne a yankin Galbi da ke a karamar hukumar Cihikun
Aruwan ya ce, dakarun sun kuma kwace wasu makamai daga gun ‘yan ta’addar da suka hada da bindigar AK47 da GPMG da babura daga mafakar ‘yan ta’addar.
Gwamnatin jihar ta kuma bayar da wasu lambobin wayar tafi da gidanka da al’ummar jihar za su ke kiran Jami’an tsaro don bayar da sahihan bayanai, wadanda suke kamar haka, 09034000060 ko kuma 08170189999