Kocin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Hansi Flick ya shirya tsaf domin tunkarar Borrusia Dortmund a wasa na biyu na kusa da na kusa da na karshe na gasar Zakarun Turai (UEFA) a filin wasa na Signal Iduna Park da ke Dortmund, kasar Jamus.
Akwai labari mai dadi da marar dadi a wajen masu goyon bayan Barcelona, labari mai dadin – dawowar dan wasan tsakiya Dani Olmo bayan shafe tsawon lokaci ya na fama da jinya, sai kuma marar dadi – samun raunin dan wasan baya na gefe Alex Balde.
- Kotu Ta Tsare Matasa 2 Kan Wallafa Bidiyon Batsa A TikTok A Kano
- Gwamnatin Kano Za Ta Sake Buɗe Makarantun Kwana 10 Don Inganta Ilimin Yara Mata
Balde ya samu rauni a wasan da Barcelona ta doke Leganes a karshen makon da ya gabata, hakan ya sa ba zai buga wasan da za a yi a gidan Dortmund ba duk da cewar ya buga wasan farko.
Hansi Flick na fatan lashe UEFA a karo na biyu a tarihinshi na horarwa, bayan da ya lashe na farko tare da Bayern Munich a shekarar 2020, hakazalika, Barcelona na gab da lashe gasar bayan shekaru 10.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp