Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a yau Laraba 16 ga wata cewa, mizanin hada-hadar tattalin arziki da aka fi sani da GDP na kasar Sin ya karu da kashi 5.4 bisa dari kwatankwacin makamancin lokacin bara a cikin rubu’in farko na shekarar 2025. A tsakanin wannan lokacin, alkaluman hukumar sun kuma bayyana cewa, mizanin ya nuna hada-hadar tattalin arzikin kasar ta kai yawan adadin kudin Sin yuan tiriliyan 31, da biliyan 875 da miliyan 800, kwatankwacin dala tiriliyan 4. 42.
Har ila yau, kamar yadda alkaluman mahukuntan suka nuna, karuwar darajar kayayyakin da masana’antu suka samar ta kai kaso 6.5 bisa dari duk dai a rubu’in farkon na bana. An samu wannan bunkasa ce cikin hanzari daga ci gaban da aka samu da kashi 5.9 a cikin watanni biyun farko. (Abdulrazaq Yahuza Jere).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp