Ƙungiyar Dattawan Arewaci ta bayyana cewa kashe-kashen da ake yi a Jihar Filato alama ce ta gazawar gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A cikin wata sanarwa da kakakin ƙungiyar, Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya fitar ranar Laraba, ya ce kashe-kashen da ake fama da su a Filato abin kunya ne ga ƙasa kamar Nijeriya.
- Bai Wa Shanu Guba: Sojoji Sun Shiga Tsakani Domin Dakile Yunkurin Ramuwar Gayya A Filato
- UEFA: Wasan Arsenal Da Real Madrid Ya Haddasa Rikici A Tsakanin Magoya Bayan Kungiyoyin A Kano
Ya ƙara da cewa Nijeriya da a da ta ke zaune lafiya yanzu ta koma wajen zubar da jini da rashin bin doka.
Ƙungiyar ta ce kashe bayin Allah da ba su ji ba ba su gani ba abu ne da bai kamata ba, kuma gwamnati ce ke da alhakin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Sun ce rashin ɗaukar mataki daga gwamnati na nuni da gazawa, kuma ba za a yarda da hakan ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp