Ministan ma’adinai da karafa, Arc. Olamilekan Adegbite, ya bayyana cewa dimbin albarkatun ma’adinai dake baje a ko’ina cikin kasar Nijeriya na da damar sanya kasar zama “mafi kyawun wurin saka hannun jari a duniya, wanda hakan zai sauya tattalin arzikin kasar.”
Ministan ya bayyana hakan ne a hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja gabanin taron makon Ma’adinan Nijeriya na shekarar 2022 da ake shirye-shiryen gudanarwa nan gaba kadan Yayin tattaunawa da manema labarai.
Adegbite ya bayyana cewa, taron makon ma’adinan Nijeriya da aka shirya gudanarwa tsakanin ranakun 1 zuwa 3 ga watan Nuwamba, 2022, a cibiyar taro ta kasa da kasa dake Abuja, wani bangare ne da ma’aikatar ta ke yi na nunawa duniya cewa, Nijeriya cike take da Ma’adanai kuma sashen ma’adinan a shirye yake don amsar masu zuba Jari.
Ministan ya kuma bayyana cewa, muhimman batutuwan da za a tattauna a taron za su hada da muhimman albarkatun ma’adinai wadanda su ne tubalin gina fasahohi wadanda da dama da su ake amfani wajen samarwa duniya makamashin zamani mai karancin cutarwa.