Ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin (MIIT) ta sanar a yau Jumma’a cewa, adadin tasoshin karfin fasahar sadarwa ta 5G na kasar Sin ya haura fiye da miliyan 4.39 a karshen watan Maris, inda adadin masu amfani da fasahar kuma ya kai kashi 75.9 cikin dari.
A yayin wani taron manema labarai da aka gudanar, babban injiniya a ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwar, Xie Shaofeng ya bayyana cewa, ayyukan samar da intanet na kasar Sin na ci gaba da inganta, kuma masana’antunta na fasahohin zamani sun hau wani sabon mataki na koli.
- Rundunar ‘Yansanda Ta Tuhumi Jami’anta Da ‘Yan Kasar Sin Ke Raba Wa Kudi A Wani Bidiyo Da Ke Yawo
- Ta Ya Ake Gudanar Da Nagartacciyar Rayuwa?
Xie ya ce, fasahohin na zamani a karkashin karfin fasahar 5G da nau’o’in samfuran kirkirarriyar basira ta AI, sun samu ci gaba cikin hanzari, yana mai cewa, fannin fasahohin na zamani ya samu karuwar kudaden shiga a mizanin shekara-shekara da kaso 8.2 cikin dari a watanni biyun farkon bana.
Kazalika, Injiniya Xie ya kara da cewa, a cikin rubu’in farko na bana, sashen masana’antu na kasar Sin ya taka rawar gani wajen samun ci gaba ba tare da tangarda ba sakamakon ingantuwar tsari da zurfafa ayyuka wajen samar da sabbin ginshikan bunkasa ci gaba mai inganci. (Abdulrazaq Yahuza Jere).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp