Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, ta bukaci ‘yan kasuwa da sauran alummar kasar nan, da su yi amfani da damar hanyoyin sauki da Hukumar ta samar wajen fitar da kaya zuwa kasar waje
Shugabanta, Dakta Abubakar Dantsoho ne, ya yi wannan kiran a cikin sanawar da Hukumar ta fitar a yayin taron baje koli karo na 36 da ta baje koli ta hada-hadar kasuwanci, masana’antu da kuma aikin noma ta jihar Enugu, ta shirya.
- Kwararru Sun Yi Musayar Ra’ayoyi Dangane Da Wayewar Kan Sin Da Afirka
- Yadda Hukuncin Kotun Koli Ya Kara Dagula Rikicin Shugabanci A PDP Da LP
“Daga cikin kokarin Hukumar na kara karfafa kasuwanici a cikin gida Nijeriya NPA ta hanyar amfani da daukaka kasuwanci, ta kafa sashen da ke samar wa masu son fiton kaya zuwa kasar waje, a cikin sauki”.
Kazalika, Dantsoho ya jaddada cewa, Hukumars, ta samar da matakan da za ta sada masu hada-hadar kasuwanci da gureren da ke wuyar shigar da kayan da musamman ake da bukatar su, a fadin duniya.
Dantsoho ya ci gaba da cewa, Hukumar ta NPA, ako wanne lokaci tana tunkaho da Cibiyar da baje kolin ta jihar Enugu, musamman duba da cewa, gudanar da hada-hadar kasuwanci shi ne, kashin bayan bunkasa tattalin arziki.
Shugaban ya kuma bai wa masu ruwa da tsaki a fannin cewa, ako da yaushe, kofar Hukumar ta NPA, bode take domin hadaka wacce ta zarce ta gudanar da baje koli.
Dakta Dantsoho ya kara da cewa, an samar da tsarin na EPT domin a tabbatar da cewa, ana fitar da kaya zuwa waje, ta hanyar yin amfani da na’urar zamani.
“Wannan na zai taimaka matuka wajen kaucewa samun jinkiri da kuma mai-maita aiki da Hukumar ta saba fuskanta a baya,” A cewar Dantsoho.
Kazalika, Dantsoho ya bayyana cewa, domin a samu sauki wajen kai kaya a tsakanin masu kananan da matsakaitan sana’oi, musamman duba da cewa, tsarin na EPT, zai taimaka matuka ga guraren da ake adana kaya a cikin kasar na, da kuma hada karfi da karfe da Hukumar Bunkasa Harkokin Fitar da Kayayyaki ta Kasa NEPC da sauran abokan hadaka.
“Domin Hukumar ta NPA ta gudnar da ayyukanta daidai da tsarin Gwamnatin Tarayya na samar da sauki ga yin kasuwanci, musamman duba da taken baje kolin na ta baje koli ta hada-hadar kasuwanci, masana’antu da kuma aikin noma ta jihar Enugu, Hukumar NPA ta samar da tsarin samar da sauki wajen bai wa ‘yan kasuwar kasar yadda za su rinka fitar da kayansu, zuwa ketare,”. Inji Dantsoho.
Shugaban ya kara da cewa, Hukumar ta kuma nasara a tsarinta na NSW, musamman duba da yadda aka samu saduwa da sauran masu ruwa da tsaki, wajen gudanar da hada-hadar kasuwanci
Dantsoho ya jinjinawa mahukunta Cibiyar ta baje koli ta hada-hadar kasuwanci, masana’antu da kuma aikin noma ta jihar Enugu, musamman kan yadda suke ci gaba da gudanar da hada-hara kasuwanci da yanyo abokan kasuwanci na cikin gida Nijeriya, da kuma na kasashen waje, wanda hakan ya kara taimakawa, wajen habaka tattalin arzikin kasar.
Shugaban ya yi nuni da cewa, duba da yadda jihar ta Enugu ta kasance a yankin Kudu Maso Gabas, hakan zai taimaka mata wajen samar da damar kara fadada fitar da kaya zuwa ketare.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp