Hukumar Kwallon Kafar Kudancin Amurka (Conmebol) ta gabatar da bukata a hukumance na kara yawan kasashen da za su halarci Gasar Kofin Duniya ta 2030 zuwa kasashe 64.
Hadakar kasashen Sifaniya da Morocco da Portugal ne za su karbi bakuncin gasar, bayan bude ta a kasashen Argentina da Paraguay da kuma Uruguay. Gasar Kofin Duniya ta 2026 ce ta farko da kasashe 48 za su halarta, to amma Conmebol na son a fadada gasar a 2030 domin murna cika shekara 100 da fara gasar a duniya.
- Kwararru Sun Yi Musayar Ra’ayoyi Dangane Da Wayewar Kan Sin Da AfirkaÂ
- Yadda Hukuncin Kotun Koli Ya Kara Dagula Rikicin Shugabanci A PDP Da LP
A cewar shugaban Conmebol, Alejandro Dominguez a wani taro da hukumar ta gudanar ranar Alhamis yin karin zai bai wa kasashen duniya damar kallon gasar, don haka ba wanda za a bari a baya dangane da bikin da za a yi na cika shekara 100 da fara gasar cin kofin duniya. Ya ce sun yarda cewa bikin cika shekara 100 na gasar zai zama na kasaitacce, saboda ba a taba yin irinsa ba.
Shugaban hukumar kwallon kafar Uruguay, Ignacio Alonso ne ya fara gabatar da bukatar a lokacin taron Fifa da aka gudanar cikin watan Maris kuma a cikin wata sanarwa da hukumar Fifa ta fitar ranar Juma’a, ta ce hakkinta ne ta yi nazarin kowace shawara da mambobinsu suka gabatar.
Shugaban hukumar ta FIFA, Gianni Infantino ya halarci taron Conmebol na ranar Alhamis, inda kuma ya bayyana cewa Gasar 2030 za ta zama ”gagaruma” da ba a taba gani ba.
A shekarar 2017, aka dauki matakin fadada kasashen da za su halarci gasar 2026 zuwa 48 bayan duka mambobin Fita sun kada kuri’ar amincewa da matakin, sannan a ranar 15 ga watan Mayu mai zuwa ne za a gudanar da taron FIFA na 75, kuma a nan ne za a tattauna bukatar ta Conmebol. Idan har aka amince da bukatar, gasar ta 2030 za ta kunshi karawa 128, daga karawa 64 da ake yi tsakanin 1998 zuwa 2022.
Masu sukar matakin dai na cewa fadada gasar zai rage darajar tsarin da ake bi wajen tantance cancantar shiga gasar, yayin da kungiyar kare muhalli ta FFF ta ce shawarar buga gasar a nahiyoyi uku barazana ce ga muhalli. Tuni dai a farkon watannan shugaban hukumar kwallon kafar Turai, Aleksander Ceferin ya bayyana matakin a matsayin ”mummunar shawara”.
Ya ce wannan shawara ta yiwu ta fi ba shi mamaki fiye da su, domin shi yana ganin wannan shawara ce maras kyau a ra’ayinsa. Za dai a fara gasar 2030 a Uruguay – kasar da ta fara lashe gasar a 1930, a wani bangare na bikin cika shekara 100 da fara gasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp