Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) sun samu nasarar damke shugaban kamfanin ‘Marvelrock Pharmaceuticals and Stores Limited,’ Mista Orakwe Chibuike Celestine, bisa sayar da miyagun kwayoyi ta kafar intanet.
Dan kasuwar, Orakwe, ya yi rijistar kamfanin ranar 16 ga watan Disambar 2014, inda ya samu lasisin sayar da magani, sannan daga bisani ya fada cikin mummunar wannan sana’a a shakarar 2017.
- NDLEA Ta Cafke Tsohon Sojan Da Ke Wa ‘Yan Bindiga Safarar Miyagun Kwayoyi
- Hukumar NDLEA Ta Bankado dakunan Sarrafa Miyagun kwayoyi A Legas Da Anambra
Wanda ake zargin ya ci gaba da gudanar da mummunan kasuwancinsa ta intanet tun daga shekarar 2019.
Mutumin ya fada komar hukumar NDLEA a watan Oktobar 2021, lokacin da ya tallata kwayoyi irin su Tramadol da Ketamine Hydrochloride injection da kwayar Hypnox flunitrazepam da dai sauransu.
Hukumar ta bayyana hakan a wata sanarwa Daraktan yada labarai na hukumar, Femi Babafemi, ya fitar a ranar 17 ga watan Agustan 2022.
A tsakanin ranar 26 ga watan Oktoban 2021 har zuwa ranar 8 ga watan Agustan 2021, jami’an hukumar NDLEA suka fara binciken, Orakwes, bisa gudanar da kasuwancin miyagun kwayoyi irinsu Tramadol da dai sauransu a intanet.
Hukumar ta dai samu nasarar damke wanda ake zargin ne a yankin Jabi da ke cikin garin Abuja a wata mashaya, inda ya je haduwa da abokan huldarsa.
Da yake tsokaci kan kame, Orakwes, shugaban hukumar NDLEA, Brig. Gen. Mohamed Buba Marwa (Retd) ya bayyana cewa hukumarsa ta gudanar da cikakken bincike kafin damke dan kasuwar kwayar. Ya ce hakan zai zama darasi ga sauran masu kasuwancin miyagun kwayoyi a intanet wajen fuskantar abin da suka girba.