Gwamnan Jihar Benuwai, Reverend Father Hyacinth Alia, ya bayyana cewa wasu maharan da suka kai hari a jihar ba ‘yan Nijeriya ba ne.
Yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Gwamna Alia ya ce irin harshen da maharan ke amfani da shi – Hausa da Fulatanci – ba irin wanda ake amfani da shi a Nijeriya ba ne.
- Rashin Jituwa Tsakanin Amurka Da China Na Iya Jefa Tattalin Arziƙin Duniya Cikin Hatsari – IMF
- Sabuwar Ƙungiyar ‘Yan Bindiga Ta Addabi Jihohin Kwara Da Neja
Ya ce: “Sun zo ne É—auke da makamai irin su AK-47 da AK-49, kuma ba sa magana kamar yadda mu ‘yan Nijeriya muke yi. Harshensu daban ne.”
Gwamnan ya Æ™ara da cewa bayanan da suka fito daga mutanen yankunan da aka kai wa hare-haren sun tabbatar da cewa maharan ba ‘yan Nijeriya ba ne.
Wannan jawabi ya fito ne bayan ziyarar da mai bai wa shugaban Æ™asa shawara kan harkar tsaro, Nuhu Ribadu, ya kai jihar domin nuna alhini da kuma tabbatar wa da al’umma cewa gwamnati na É—aukar matakai don shawo kan matsalar tsaro.
Ba wannan ne karon farko da ake zargin wasu ‘yan Æ™asashen waje da kai hare-hare a Nijeriya ba.
A baya an yi zargin cewa ƙungiyoyi kamar Lakurawa da ke kai hare-hare a jihohin Sakkwato da Zamfara, sun samo asali ne daga ƙasashen waje.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp