Hukumar lura da gidajen bashin ma’aikatan gwamnatin tarayya (FGSHLB) ta sanar da cewa ta fara tattara jerin sunayen ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya amma ba su biya bashin gidajen da suka karÉ“a ba.
Shugabar sashin sadarwa da hulÉ—a da jama’a na FGSHLB, Ngozi Obiechina, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis a Abuja, inda ta ruwaito cewa shugabar hukumar, Salamatu Ahmed, tana cewa wannan matakin yana nufin dawo da dukiyoyin da aka yi rance daga ma’aikatan da suka yi ritaya amma ba su kammala biyan bashin ba.
- Rashin Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Saka Dokar Zama A Gida A Minna
- Gina Al’umma Mai Kyakkyawar Makomar Bai Daya: Jigon Ziyarar Xi A Kudu Maso Gabashin Asiya
Salamatu Ahmed, ta bayyana cewa wannan hukuncin ya biyo bayan wanta takardar saÆ™o da sakatariyar dindindin ta ofishin gudanar da ayyukan ma’aikatan gwamnati, Patience Oyekunle, ta fitar. Ta ce takardar ta tunatar da ma’aikatan gwamnati kan bukatar samun takardar shaidar bashi da ba a biya ba daga FGSHLB da MDA Staff Multipurpose Cooperative Society a matsayin sharadi na yin ritaya, tana mai cewa hukumar za ta dauki matakai na shari’a don dawo da dukiyoyin idan an samu da wasu da karya yarjejeniyar bashin.
Ta kuma kara da cewa wannan matakin yana cikin ka’idojin dokokin ayyukan gwamnati na 021002 (p) da Ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati na tarayya ya fitar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp