Fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, zai angwance da jarumar Kannywood, Aisha Humaira.
Wata majiya mai kusanci da Rarara ta shaida wa jaridar Kano Times cewa za a ɗaura auren ne gobe Juma’a a Maiduguri, a Jihar Borno, bayan sallar Juma’a.
- Uwargidan Shugaban Kasar Sin Ta Tattauna Da Takwararta Ta Kasar Kenya
- Baffa Bichi, Kabiru Rurum, Sha’aban Sharada Da Wasu Sun Koma Jam’iyyar APC
“Komai ya kammala. Za a yi auren da yardar Allah,” in ji majiyar.
Rarara da Aisha sun daɗe suna aiki tare, kuma alaƙarsu ta ƙara ƙarfi har ta wuce iya aikin waƙa kawai.
A cewar wasu da ke kusanci da su, wannan aure ba abin mamaki ba ne.
“Aisha ba wai mawaƙiyar amshi ba ce kawai a wajen Rarara ba. Sun yi matuƙar shaƙuwa da juna, kuma mu da muka san su ba abin mamaki ba ne don an ce za a yi wannan aure,” in ji majiyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp