Duk da hukuncin kotun koli da ta ba da umarnin biyan kason kai tsaye ga kananan hukumomi, gwamnatin tarayya ta ba da naira tiriliyan 1.232 ga kananan hukumomi a farkon kwata na 2025 ta hannun gwamnatocin jihohi, tun daga lokacin da aka jinkirta hukuncin.
Binciken bayanan da kwamitin raba asusun tarayya ya fitar ya nuna cewa kananan hukumomi sun karbi naira biliyan 434.57 a watan Janairu, naira biliyan 410.56 a watan Fabrairu, da kuma naira biliyan 387 a watan Maris, jimillar naira tiriliyan 1.232.
Rabon kudaden yana wakiltar kashi 24.8 cikin 100 na naira tiriliyan 4.959 da aka raba tsakanin matakan gwamnati uku a cikin ruba’in wannan shekara.
A watan Janairu, kwamitin ya raba naira tiriliyan 1.703 tare ga gwamnatoin tarayya da jihohi da kananan hukumomi. A wannan kudade, gwamnatin tarayya ta karbi naira biliyan 552.59, jihohi sun karbi naira biliyan 590.61, yayin da kuma kananan hukumomi sun karbi naira biliyan 434.57.
Rabon kudaden ya dogara ne kan kudaden shiga na naira biliyan 749.73, harajin BAT naira biliyan 718.78, harajin canja wurin kudi ta hanyar lantarki na naira biliyan 20.55, da kuma karin naira biliyan 214.
Rabon watan Fabrairu ya kai naira biliyan 1.678, inda gwamnatin tarayya ta karbi naira biliyan 569.66, jihohi sun karbi naira biliyan 562.20, sannan kuma kananan hukumomi sun sami naira biliyan 410.56.
Kudaden shiga sun hada da naira biliyan 827.63 na kudaden shiga na doka da naira biliyan 609.43 daga VAT da naira biliyan 35.17 daga EMTL da naira biliyan 28.22 daga ma’adanai da karin naira biliyan 178.
A watan Maris, kwamitin ya raba naira tiriliyan 1.578. Gwamnatin tarayya ta karbi naira biliyan 528.70, jihohi sun karbi naira biliyan 530.45, sannan kuma kananan hukumomi sun karbi naira biliyan 387.
Kudaden shiga da aka rarraba sun hada da naira biliyan 931.33 a cikin kudaden shiga na doka da naira biliyan 593.75 daga harajin BAT da naira biliyan 24.97 daga EMTL, da naira biliyan 28.71 daga musayar kudade.
Kudaden shiga daga VAT a watan Janairun 2025 ya kai na naira biliyan 771.89, ya ragu zuwa naira biliyan 654.46 a watan Fabrairu da naira biliyan 637.62 a Maris. A halin yanzu, kudaden shiga na doka ya karu daga naira tiriliyan 1.848 a watan Janairu zuwa naira tiriliyan 1.653 a watan Fabrairu da naira tiriliyan 1.718 a watan Maris.
Duk da wadannan karin kudaden shiga, har yanzu kananan hukumomi ba su fara amsar kudadensu kai tsaye ba daga asusun tarayya, sabanin umarnin kotun koli da ta bayar a watan Yulin 2024.
Kotun koli ta ba da umarnin a biya kudaden kananan hukumomi daga asusun tarayya kai tsaye don tabbatar da ‘yancin cin gashin kansu na kudi da kuma kare su daga tsoma baki daga gwamnatocin jihohi.
Kungiyar kananan hukumomi ta Nijeriya (ALGON) ta zargi ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya da kawo cikas ga aiwatar da ‘yancin cin gashin kai na kananan hukumomi, duk da cewa kotun koli ta yanke hukunci kan bayar da kudaden kai tsaye ga dukkan kananan hukumomi 774 da ke kasar nan.
ALGON ta kuma dauki matakin shari’a a kan babban lauyan gwamnatin tarayya da wasu cibiyoyin tarayya da dama a karar mai lamba ta FHC/ABJ/05/353/2025, suna nemanbai wa kananan hukumomi cikakken ‘yancin sarrafa kudadensu da kansu.
Karar ta kuma hada har ministan kudi, Wale Edun da ministan kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Abubakar Bagudu da akanta janar na tarayya da CBN da NNPCL da kuma bankunan kasuwanci a matsayin wadanda ake tuhuma.
ALGON ta ce ta dauki wannan matsayin a kotu ne da nufin ba kawai tilasta ‘yancin gashin kai a takarda ba har ma da tabbatar da aiwatar da shi.
Shari’ar wacce da farko aka shirya yi a gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo, amma kotun ba ta samu zama ba. An dage shari’ar zuwa ranar 29 ga Mayu, 2025.
Da yake mayar da martani, Sakatare Janar na ALGON, Mohammed Abubakar, ya nuna takaicinsa kan ci gaba da jinkirin biyan kudaden kananan hukumomi kai tsaye duk da hukuncin kotun koli.
Abubakar ya ce lamarin ya zama mai rikitarwa kuma yawancin ‘yan Nijeriya sun yi takaicin faruwar hakan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp