• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Babu Nasara Ga ’Yan Awaren Taiwan

by CMG Hausa
3 years ago
Taiwan

Bisa dukkanin shaidu da dalilai na zahiri, ’yan a waren yankin Taiwan na kasar Sin, da masu mara musu baya daga ’yan siyasar kasashen yamma, ba su da wani buri da ya wuce jefa Taiwan cikin yanayi na rudani. 

Lura da hakan ne ma ya sanya mahukuntan kasar Sin dukufa matuka, wajen yin aiki kafada da kafada da masu burin ci gaban tsibirin Taiwan, wajen shawo kan duk wasu batutuwan da suka shafi sake dinkuwar yankin da babban yankin kasar Sin cikin lumana.

  • Wani Mutum Ya Yanke Marainansa Yana Barci, Ya Dauka Nama Ne A Ghana

Ko shakka babu, aiwatar da wannan manufa ta hanyar nacewa salon kasa daya tsarin mulki biyu, shi ne mataki mafi dacewa na dinkuwar kasar Sin cikin ruwan sanyi, amma kuma duk da haka, ya kamata masu son gurgunta wannan manufa su san cewa, gwamnatin kasar Sin ba za ta bar duk wata kafa ta cimma nasarar ’yan a ware ba.

Bisa goyon bayan daukacin al’ummun kasar Sin, da kudurorin MDD masu nasaba da hakan, da ma goyon bayan sauran sassan kasa da kasa, batun dinkuwar yankin Taiwan na da tushe na dokar kasar Sin, da ma dokokin cudanyar kasa da kasa.

Kaza lika bangarorin da suka ki amincewa da hakan, suna kokari ne na tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, da yunkurin gurgunta moriyar kasar da ikon mulkin kanta.

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

Sanin hakan ne kuma ya sanya gwamnatin kasar Sin ta shirya tsaf, domin tunkarar duk wani shiri na amfani da batun Taiwan, don tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar. Hakan tamkar kashedi ne, da jan kunnen masu ganin za su iya keta hurumin ikon mulkin kai na kasar Sin. Domin kuwa Sin na da ikon amfani da dukkanin hanyoyi mafiya dacewa, na kare kai daga barazanar makiya.

Bahaushe kan ce “Idan kunne ya ji jiki ya tsira”, wato dai bayanai da mahukuntan kasar Sin ke fitarwa, da matakai na zahiri da gwamnatin kasar ke dauka, na tabbatar da cewa, ’yan a waren yankin Taiwan, da masu mara musu baya daga ’yan siyasar kasashen yamma, ba za su taba yin nasarar cimma mummunar manufar su ba! (Saminu Hassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 24, 2025
Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa
Daga Birnin Sin

Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

October 24, 2025
Next Post
Xi Jinping Ya Yi Rangadin Aiki A Birnin Shenyang

Xi Jinping Ya Yi Rangadin Aiki A Birnin Shenyang

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

October 25, 2025

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

October 25, 2025
Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange

Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

October 25, 2025
Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa

October 25, 2025
Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi

October 25, 2025
Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.