Domin auna kwazon gwamnatin Donald Trump a wa’adin aikinsa na wannan karo, kafar CGTN ta kasar Sin ta yi hadin gwiwa da jami’ar Renmin ta kasar, inda suka gudanar da kuri’un jin ra’ayin jama’a tsakanin watan Fabairu da Afirilun da ya gabata, ta cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa a sabon zamani, sakamakon binciken ya fayyace ra’ayoyin mutane 15,947 daga kasashe 38.
A game da manufar da gwamnatin Amurka ta dauka ta “Amurka gaban komai”, kaso 65.1 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin na ganin manufar ta yi matukar gurgunta matsayin Amurka na jagorancin kasa da kasa, adadin da ya karu da kaso 15.3 bisa dari cikin watanni 2. Kazalika, kaso 87 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyinsu daga kasar Koriya ta Kudu, na ganin manufar “Amurka gaban komai” za ta tilasawa Amurka yin watsi da kawayenta. Kana sama da kaso 70 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi daga kasashen Birtaniya, da Jamus, da Canada, da Australia da Italiya su ma sun amince da hakan.
A daya hannun kuma, cikin kasashe kawayen Amurka, kaso 65.5 bisa dari daga Australiya na da karancin kwarin gwiwar bunkasar alakar kasarsu da Amurka, adadin da ya nuna karuwar kaso 24.5 bisa dari na hakan cikin watanni 2. Sai kuma al’ummun Italiya da ke kan wannan matsaya da suka kai kaso 55 bisa dari, karuwar da ta kai kaso 21.5 bisa dari.
Cikin masu bayyana ra’ayoyin na kasashen duniya masu tasowa 23, 19 wato kaso 82.6 bisa dari sun rasa kwarin gwiwa game da kyautatuwar alakar kasashensu da Amurka. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp