Wuta ta tashi da safiyar yau Juma’a inda ta ƙone shaguna uku da wasu kayayyaki masu yawa a unguwar Sango da ke cikin babban birnin jihar Oyo, Ibadan. Manaja Janar na hukumar kashe gobara ta Jihar Oyo, Akinyemi Akinyinka, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa wutar ta tashi a bayan wani gidan man da ke Sango.
Akinyinka ya ce an ba da rahoton faruwar gobarar da karfe 4:41 na safe ta wayar tarho, kuma ma’aikatan hukumar, ƙarƙashin jagorancin ACFS Adedeji (Mrs.), sun isa wurin nan da nan. “Lokacin da muka isa, mun gano cewa shaguna uku daga cikin goma na shagunan sun ƙone. Mun yi sauri mu kawar da wutar kuma mun hana ta yaɗuwa zuwa sauran shaguna,” in ji shi.
- Gobara A Haramtacciyar Wurin Ajiye Man Fetur Ta Ci Rayukan Mutane 5 A Jihar Ribas
- Gobara Ta Tashi A Barikin Sojoji A Borno, Bama-bamai Sun Fashe
Ko da yake ba a sami rahoton asarar rayuka ba, amma wutar ta lalata shaguna uku, da Firinji, da abubuwan sha. Akinyinka ya bayyana cewa wutar ta fara ne sakamakon wutar da ta fito daga firiji da aka sa a cikin shagon, wanda ya ƙona wasu abubuwa masu saurin kamawa kafin ya mamaye shagunan.
Ma’aikatan kashe gobara sun ceci wasu shaguna da kayayyaki da darajarsu ta kai miliyoyin Naira.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp