Tsohon shugaban gudanarwa na Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), Engr. Mele Kyari, ya mayar da martani kan zargin binciken da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) aka ce tana yi akansa.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, EFCC ta kaddamar da bincike akan wasu tsofaffin jami’an kamfanin NNPCL a matakin gudanarwa da na matatun mai a Warri, Kaduna da Fatakwal.
- Ko Kin San… Yadda Ake Nagartaccen Tsumi?
- Gwamnatin Nijeriya Ta Goyi Bayan Amfani Da Ƙirƙirarrar Basira Cikin Ɗa’a A Aikin Jarida – Minista
Sai dai kuma da yake mayar da martani ga wannan yunkuri, Kyari ya musanta cewa, yana tsare a hannun hukumar EFCC, inda ya yi fatali da ikirarin da cewa, “ba Nijeriya kadai na yi wa aiki ba, na hada har da tsoron Allah a tsawon shekaru sama da 30 da na yi ina aiki a NNPC”.
Kyari ya mayar da martani ne a shafinsa na X a daren ranar Asabar 3 ga watan Mayun 2025.
Wata jarida ta yanar gizo ce ta yi ikirarin cewa, Mele Kyari yana tsare a hannun EFCC domin amsa tambayoyi game da zarge-zargen almundahana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp