Shafin TASKIRA shafi ne daya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya da dai sauransu.
Tsokacin mu yau zai yi duba ne game da abin da ya shafi musgunawa ‘ya’ya wanda iyaye mata ke yi. Wasu daga cikin iyaye mata suna gallaza wa ‘ya’yansu na cikinsu, don ganin sun bakantawa mazajensu rai musamman idan suka samu sabani da juna, ko ya hana wani abun wanda ba sa so a hana su.
Dalilin hakan ya sa muka ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batun “Me za a ce a kan hakan?, wane amfani yin hakan yake da shi?, ko akwai wata matsala da hakan zai iya haifarwa?”
Ga dai bayanan nasu kamarhaka:
Sunana Princess Fatimah Mazadu Daga Jihar Gombe:
A gaskiya wannan matsalar takan faru ne a tsakanin ma’auratan da basa son juna sosai, hadin gida (auren dangi), ko babbar matsala na karya alkawari tsakaninsu, abu ne kuma wanda bai kamata ana yi wa yara hukuncin da ba laifinsu, wannan a bayyane cin zali ne da shirin maida yaro kangarerre. Ba shi da wani amfani sai illah, dan ya kan maida yaro ya zamo baya tausayin iyayenshi, kullum yana cikin jimamin rayuwarsa a duk sanda iyayensa suka samu sabani to, a kanshi ko a kansu za a huce haushi. Babbar matsala ma, dan zai sanya kokwanto a zuciyar yaransu na cewa iyayen nasu anya suna sonsu kuwa? Ko su kadai Allah ya bawa irin wadannan iyayen?, za su kasance suna turrr da halayen iyayen da irin rayuwar da Allah ya jarabcesu da shi. Shawara daya ce a duk sanda maaurata suka samu sabani kar su bari zuciyarsu ta ja su ga bakantawa yaransu dalilin nasu bakin cikin, su kiyaye sauke takaicinsu a kan yaransu dan watarana zuciya za ta kaisu ta bari cike da da-na-sani, dan basu san irin raunin da watarana za su yi wa yarannasu ba, gwargwadan bacin ransu gwargwadon illar da za su yi wa yaransu, Allah ya kare mu da wanann zuciyar ya kuma shirya mu ya shirya mana zuriya.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Jihar Kano Rano LGA:
Abin da hakan ke nufi hauka da rashin sanin yakamata. Ba shi da amfani sai rashin amfanin kansa domin na farko ta dauki alhakin yaransu, sannan kuma hakan sai dai ya kara tunzura maigidan. Babba ma kuwa domin idan uwa ta sake wannan ya zama al’adarta to ta sani watarana za ta iya rasa aurenta ko kuma ta rasa biyayya daga yaron da ake gallazawa da zarar ya gano abin da yake faruwa domin shi uban kansa zai iya dinga jawo yaron a jikinsa har sabon da yayi da mamansa ya koma kan uban. Shawarata a nan ita ce gaskiya su guji irin wannan halin da dabi’ar domin shi fa zagin iyaye ko muzgunawa yaro da iyaye suke yi baki suke wa yaro ba wai sai sun ce Allah yayi wadaran yaro ba kun ga kenan yaro tun yana karami mamansa ta jawo masa aibu tun yana karami bai ji ba bai gani ba don haka gaskiya mu iyaye muna sanin abin da za mu dinga furtawa yaranmu ko da ya ki ne ya faru tsakanin iyayensa din ba ma wani sabani ba. Allah ya kyauta ya shirya mana zurya amin.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To hakika iyaye masu irin wannan dabi’a ko hali suna kuskure ne, kuma wannan kuskuren da suke zai bibiye su har karshen rayuwar su, domin dalilin wannan gallazawa da suke tana haddasa kiyayya a tsakaninsu da yaran ta har abada. Babu wani amfani domin shi fa yaro ba shi yayi laifi ba, kuma ita ma danta ne ba wai na uban ne shi kadai ba, don haka bai kamata ta musguna masa ba, saboda wai don ta rama abun da ubansa yayi mata sam-sam bai dace ba. Sosai ma kuwa, domin kuwa cigaban da yin hakan zai iya haifar da tsana a tsakanin ta da yaron kuma shi uban yaron za ta fita daga ransa wanda hakan ka’iya jawo mutuwar aure ko kuma rashin mutunta juna a zamantakewar aure. To ni dai shawara ta a nan ita ce ya kamata iyaye suna kokarin magance matsalar zaman takewar su ta aure a tsakaninsu ba tare da sa ‘ya’yansu a ciki ba, domin hakan zai taimaka wajen cigaba da zama tare da juna da samun hadin kai a tsakanin iyalai.
Sunana Hafsat Sa’eed Daga Jihar Neja:
Ni dai a nawa tunanin idan ka yi haka dan ka batawa maigidan rai ba abu ne me amfani ba kuma babu fa’ida a cikin hakan, tunda kuwa kai ka haifi danka da cikinka yadda ka ji ciwon haihuwarshi shi mijin bai ji ciwon ba, wani namijin ma babu ruwanshi dan kin gallazawa danki. Matsalar da hakan zai iya haifarwa shi ne; yaron zai ji tsanar uwar a ransa. Shawarata ya kamata duk abin da namiji zai yi miki to, ya tsaya tsakaninki da shi.
Sunana Muktari Sabo Jahun A Jihar Jigawa:
Hakika wannan tana faruwa a tsakanin ma’aurata kuma ana yin hakanne don munanawa daya barayin wanda hakan ba dai dai bane. Yin haka ba shi da wani amfani karshe ma matsala yake haifarwa a tsakanin ma’aurata ko kuma tsakanin yara da iyayensu. Tabbas hakan yana haifar da matsala domin yana kawo sabani tsakanin ma’aurata wanda har yana iya zama sanadin auren sannan kuma yana kawo kiyaiya tsakanin yara da iyayensu. Shawara a nan ita ce iyaye mata su ji tsoron Allah su daina aikata hakan domin laifin wani baya shafar wani.
Sunana Idris Haruna Zareku Miga A Jihar Jigawa:
A kan wannan batun, ana iya cewa iyaye da suke gallazawa ‘ya’yensu suna gudanar da abin kunya da rashin tausayi, wannan na iya haifar da matsaloli masu yawa ga ci gaban yara, tun daga damuwa da rashin jin dadin jiki har zuwa rashin yarda da kai. Abubuwan da zai iya zama amfaninsa za a iya ganin gallazawa a matsayin hanyar koyar da ‘ya’yansu darussa na tarbiyya da zama masu biyayya da jimrewa a cikin al’umma. Gallazawa na iya haifar da damuwa da rashin jin dadi ga ‘ya’yan, wanda zai iya shafar ingancin huldar su da iyayensu. Sannan hakan na iya haifar da rashin yarda tsakanin ‘ya’ya da iyayensu, wanda zai iya janyo rashin zaman lafiya a cikin iyali. Shawarwari ga iyaye mata da su yawaita tattaunawa tare da ‘ya’yansu, su saurari ra’ayoyinsu da jin damuwarsu, su yi kokarin gina amincewa da ‘ya’yansu ta hanyar kyakkyawar gwaninta da goyon baya, maimakon matsin lamba. Su fahimci cewa bai dace ba su rika hargitsa ‘yanu’wansu domin abubuwan da ba su ji dadin su ba, sai dai kyautata hanyar da za su koyar da su kyawawan dabi’u.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp