An yi nasarar kammala bikin baje kolin kayayyakin shige da fice wanda aka fi sani da Canton Fair wanda aka gudanar a zahiri a ranar 5 ga watan Mayun nan a a birnin Guangzhou.
Ya zuwa ranar 4 ga Mayu, jimillar masu sayayya 288,938 na ketare daga kasashe da yankuna 219 ne suka halarci baje kolin, adadin da ya karu da kashi 17.3 cikin dari idan aka kwatanta da na baje kolin Canton Fair karo na 135. Cinikin kayayyakin fice da aka yi niyya a filin baje kolin ya kai dalar Amurka biliyan 25.44, karuwar kashi 3 cikin dari.
Bayan rufe baje kolin Canton Fair na bana, dandalin baje koli na yanar gizo na Canton Fair zai ci gaba da aiki kamar yadda aka saba a duk shekara. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp