Barkanmu da sake saduwa daku a wannan filin namu, a wannan makon mun kawo muku ra’ayoyinku ne a kanj yadda ake samun hauhawar farashin kayan masarufi a Nijeriya, shin, yaya take ne a yankunan ku?
Yahaya Aliyu Sani
To abin dai yawuce tunanin mu sai dai mu yi ta addu’a domin ganin canji
Adam Ajiya
To ba abin da za mu ce sai innalillahi wa inna ilaihirrajiun don abin ya fi Karfin tunanin dan adam, komai Kara hawa yake, wani abinma wallahi kawai sharrin ‘yan kasuwa ne sai a fakeda shuwagabanni to Allah mun tuba ka yafe mana ka kawo mana sauKin lamurra
It’z Sam Dambatta
To Babu abin da za mu ce sai dai mu yi wa Allah godiya domin kuwa a sakamakon sabonn amfanin gona ya kusa zuwa gida, wanda suka sayi abinci suka boye sun fara fito dashi a sanadiyar hakan da yawa daga cikinsu farashin ya fara raguwa sai dai fatan Allah ya sa a tafi a haka
Khadija Muhammad
Sai hamdala al’amarin ya wuce hankali domin karin ya zama kullum da safe da yamma abinda na fahimta shi ne har da mugunta irin tamu, Allah ya shiryar da mu mu daina cutar da juna
Idris Saminu Shuaibu
Gaskiya maganar hauhawar farashi na kayayyaki abin ba a cewa komai yau idan kana da jarin dubu 10 to gobe da ka koma kasuwa zai zama na dubu 8 ko kasa da haka kullum kaya Kara tsawwalewa suke sai dai mu yi addu’a Allah ya kawo mana dauki kuma mu gyara halayen mu
It’z Jameel Moh’d
Gaskiya a yankinmu babu sauKi kawai dai addu’a muke yi kullum Allah ya kawo mana dauki cikin sauKi, ga matsalar tsaro ga hauhawar kayan masarufi, dame talaka a wannan Kasar zai ji
Lami S Mudu
Abin sai dai godiyar Allah, amma ai maganar hauhawar kayan masarufi ruwan dare ne game duniya, muna roKon Allah ya kawo mana sauKi a cikin al’amarin ya ba mu abinda zamu tsaya akai
Fa’izah Muhammad Sajo
Abin ba a Magana, yanzu mamana ta dawo kasuwa komi ya tashi a nan kasuwar Kawo da ke Kaduna
Bashir Ibrahim Matazu
Abin sai dai addu’a, Bredin din da nake Saya 450 a 2020 Yanzu Ya koma Naira 1,000 abin sai addu’a kawai, Allah Ya hore mana abin siya, amin.
Abubakar Muhammad Kirfi
Anan Gombe babu sauKi cutar arne
Hussain SO Sartsen Zuci
Ruwan dare ne ya shafi ko ina, abin kam ba sauKi sai dai daga wajen ALLAH.
Abdulmumini Sese
Gida ya tsaya chak
Fatima Ibrahim Mukhtar
Ba sauki ko digo a nan Ikko
Adamu Yunusa Ibrahim
Bahaushe ya yi gaskiya da ya ce “Idan an bi ta barawo, sai a dawo a bi ta mai bin sawu”. Da yawa ‘Yankasuwarmu na da hannu dumu-dumu wajen hauhawar farashin kayayyakin masarufi a Arewacin Nijeriya in da na fi sani. Mutane na da mummunar dabi’ar sayen kayan amfanin gona, a lokacin girbi suna boyewa, sai ya yi tsada a fito da shi. Ko shakka babu wannan na daga cikin dalilan da ke sa wa, kayan amfanin gonar yin tashin gwauron zabo a kusan dukkansu Kasar.
Haka kuma rashin tsari mai kyau daga Gwamnati shi ma yana taka muhimmiyar rawa, wajen kawo tsadar masarufi. Yakamata Gwamnati ta yi dayan hudu.
A. Ko dai ta samar da tallafi a kan kayan masarufin ta hanyar bayar da bashi maras ruwa ga manoma, kuma idan sun noma ta saya da tsada, sannan ta karya shi a kasuwa domin Talakawa marasa Karfi su amfana. Idan aka yi haka za a samu amfani kusan biyar. Na farko dai an taimaki manoman wajen samar musu da bashin da babu ruwa. Na biyu, an sake taimakar manoman ta hanyar sayen kayan amfanin gonar da daraja. Haka kuma an taimaki marasa Karfi, domin za su samu abinci a rahusa. Hakan zai bayar da natsuwa da kwanciyar hankali a Kasa. Sannan uwa zai bunKasa tattalin arzikin Kasa, da na jama’a.
B. Idan haka ba za ta samu ba, Gwamnati ta shiga harkar noma gadan-gadan. Wato, ta nemi gonaki da za ta zuba kudi ta yi noman rani da na damuna, sannan ta rika sayar wa da Talakawa da sauKi.
C. Idan haka ba ta samu ba, Gwamnati na iya bude bodojin Kasar, ta yadda za a samu a riKa shigo da abinci daga maKwabta. Wanda hakan zai samar da gasa a tsakanin kamfanonin shigo da abinci. Idan aka samu gasa, dole za a samu sauKi. Domin idan wannan ya tsawwala, tabbas wancan zai sauKaKa. Hakan zai sa a samu sauKi.
D. Ko kuma ita Gwamnatin ta riKa shigo da abincin daga Kasar waje, tana sayarwa da Talakawa a kudi mai rahusa.
Idan aka dauki daya daga cikin wadancan matakan tabbas abinci zai wadata, kuma zai yi sauKi. Domin tsakani da Allah, mutane na cikin damuwa a kan yadda kayan masarufi ke neman gagararsu. Domin duk abin da ka saya yau a Kasuwa, gobe idan ka koma sai an Kara wani abu a kai. Babu zancen sauKi.
Comrade Adamu Yunusa Ibrahim,
Malami a Cibiyar Nazarin Hausa,
Jami’ar Usmanu Danfodiyo,
Sakkwato, Nijeriya.
SadeeK Rufa’i Banguguwa
Allah yana cewa:”ArziKinku yana sama hakanan abinda ake muku alKawari da shi”
Lalle cikin wadannan kwanaki ana fama da tsadar kayan masarufi, da hauhawar farashi musamman kuma a wannan Kasa tamu Nigeria, rayuwa tana neman ta gagari mutane da yawa.
Sai dai mu sani hakan na faruwa ne da nufin Allah, domin shi ne mai sanyawa komai farashi, kuma mai shimfida arziKi mai damKe shi, kamar yadda Annabi ya fada a cikin hadisin da Muslim ya rawaito.
don haka mu rika tunawa da wannan, mu fahimci cewa ana jin dadi ne sanda Allah ya yi nufi a sha wahala sanda yai nufi.
An ce da Ibrahim Dan Adhama: “Farashi ya tashi sai ya ce : “Idan da alkama daya za ta zama Dinare daya ake saida ita hakan ba zai dameni ba, wajibin da ke kaina na bautawa Allah kamar yadda ya umarce ni, Shi kuma zai azurtani kamar yadda ya yi alKawari” Allah ta’ala yana cewa: “Ban halicci Aljanu da Mutane ba, sai domin su bauta min, bana neman arziki daga wajensu, bana neman su ciyar da ni, lalle Allah shine mai azurtawa kuma mai karfi.
Allah ka bamu abinda za mu sayi abinda muke buKata, ka yalwata mana arzikin mu. Amman tabbas akwai matsalar hauhawar farashi a wannan lokacin, sai dai in muka mika lamarinmu ga Ubangijunmu sai ya taimakemu.
SadeeK Rufa’i Banguguwa.
Hon Hafeez KiiDo
Jiya da aka gaya min kudin man gyada kwalba daya saida na nemi inuwa na zauna. A baya har 200 na siya mai kwalba, Karshen tsadarsa ya zama 400+, amma kwatsam sai ji na yi ana cewa wai ga 1,100 a siyo mai kwalba daya. Na girgiza.
Sai dai haka yawancin abubuwa suka koma, don ko Taliya da nake siyan katan 2,200 a yanzu haka naira 7,800 nake siyanta. Haka komai ya ninka kansa sau kamar uku ko hudu. HaKiKa ana shan wahala sosai, kuma duk da haka babu Karin albashin ko sisi ga ma’aikata