Baya ga fasahohin sadarwa da binciken sararin samaniya da tauraruwar kasar Sin ke ci gaba da haskawa a kai a duniya, sashen aikin gona na kasar shi ma ba a bar shi a baya ba, inda yake ci gaba da samun habaka da bullar sabbin fasahohi na zamani.
Kasancewar a halin yanzu manoma Sinawa sun dukufa ga aikin gona, sabbin fasahohin zamani da ake kara ingantawa na kara musu kwarin gwiwa da kaimin gudanar da aiki cikin sauki don kara samun girbi mai albarka. Daga cikin fasahohin, akwai wata na’ura mai tashi sama ko jirgi mara matuki da aka kera samfurin DJ1 T100 da ke iya daukar maganin feshin kwari mai nauyin kilogiram 150 wadda aka yi amfani da ita a wata makekeyar gonar alkama da ke gundumar Gaochun a Nanjing dake lardin Jiangsu a gabashin kasar Sin.
- Ministan Ilimi Ya Ce Hana Satar Amsa Ne Ya Sa Ɗalibai Suka Faɗi JAMB A Bana
- Xi Na Kan Hanyar Kai Ziyarar Aiki A Rasha
Shugaban manoman yankin, Wei Qing, ya ce na’urar tana amfani da wata fasaha dake iya tantance duk wurin da aka tura ta a cikin gona tare da fesa magani yadda ake bukata ba tare da tangarda ba. Hukumar aikin gona da raya karkara ta birnin Nanjing ta ce birnin yana da na’urori masu tashi sama dake rigakafin abubuwa masu cutarwa ga shuka, da zuba taki, da sauran ayyukan gona makamanta fiye da 1000.
Haka nan, a birnin Changsha dake tsakiyar kasar Sin, masu bincike sun kera wata na’ura ta tantance irin shuka wacce take taimaka wa manoma wajen gano sahihanci da ingancin iri. Shugaban Makarantar Kimiyyar Aikin Gona ta Hunan, Yu Yinghong ya bayyana cewa, na’urar tana aiki a matsayin raba-gardama a kan irin da za a shuka. A baya, manoma ba su gane ingancin irin shuka har sai bayan ya tsiro, amma wannan yanzu ya zama tsohon yayi sakamakon kera wannan na’ura da kasar Sin ta yi wadda ta zamo irinta ta farko a duniya.
Gane sahihancin irin shuka da yake sa tsiro ya yi yabanya sosai na taka muhimmiyar rawa wajen samun girbi mai albarka, don haka wannan na’ura take da matukar muhimmanci, kana tana taimaka wa manoma su fahimci irin shukan da ya dace da yanayin yankinsu kamar yadda wani masanin ilimin injiniyancin aikin gona, Bai Lianyang ya bayyana.
Kazalika, ana ci gaba da ganin bullar fasahohin kula da gonaki ta manhajojin zamani wadanda suke sa manoma sanin halin da gonakinsu ke ciki a duk inda suke. Wani manomi dake garin Taihe a gundumar Fuyang dake lardin Anhui na gabashin kasar Sin, Chang Xinduo ya bayyana farin cikinsa game da amfani da manhajar kula da gona ta “smart agriculture cloud” wacce ta sanar da shi dirar fararen gizo-gizo da kwarin tsanya a gonarsa ta alkama, inda nan da nan ya aike da na’urar feshi mai tashi sama ta fatattake su daga gonar mai fadin ma’aunin hekta 213.
Yanzu haka dai, a garin na Taihe kawai, an samar da cibiyoyin kula da halin da gonaki ke ciki guda 20 wadanda suke iya karade gonakin alkama masu fadin ma’aunin hekta miliyan 10.14.
Ina da yakini, idan gwamnatocinmu na Afirka suka nakalci amfani da sabbin fasahohin zamani na aikin gona kamar yadda kasar Sin ke yi, sannu a hankali ba da garaje ba, girbin da manomanmu ke yi za ta zama mai albarka ninkin-ba-ninki. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp