Mai Magana da yawun TNN, Dakta Mohammed Adah Shaibu, ya bayyana cewa ana kara yi wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) matsin lamba daga manyan bangarori daban-daban don ka da a yi wa TNN rajista a matsayin jam’iyyar siyasa a Nijeriya.
A cikin wata sanarwa da aka gabatar wa manema labarai da mai magana da yawun TNN ya rattaba hannu a Kaduna, ya bayyana cewa kungiyar ta nemi yin rajista na zamowa jam’iyyar siyasa tun a shekarar 2024.
- ICPC Za Ta Binciki Jami’an INEC Kan Almundahana A Zaben Gwamnan Edo
- Majalisa Za Ta Binciki INEC Kan Jinkirin Gudanar Da Zaben Cike Gurbi
A cewar sanarwar, an gabatar da bukatar yin rajista ga INEC kuma an amince da ita tun ranar 27 ga Mayun 2024.
Ya nuna takaicinsa cewa, “Tun lokacin da aka gabatar da bukatar yin rajista, INEC kawai ta rubuta wasikar amincewa tana alkawarin sanar da su lokacin da za a bude yi rajista don gabatar da takardu, kuma duk kokarin da aka yi don tunatar da Shugaban INEC, Farfesa Yakubu Mahmoud game da kundin tsarin mulki da dokar zabe suka tabbatar ya yi watsi da shi, duk da cewa an wuce wa’adin kwanaki 90, lokacin da aka tilsata wa hukumar mayar da sakon kan wasikar da aka shigar mata.
“Har yaushe za mu jira kafin mu yi rajista? Kasancewar mu a duk fadin kasar nan kuma muna da karancin lokaci don isar da manufofinmu na siysa ga masu jefa kuri’a.
“Babu shakka cewa INEC na fuskantar matsin lamba mai tsanani, daga mambobin APC da sauran abokan huldarsu wadanda ke tsoron TNN, domin sun shirya yin magudi a zaben 2027 wajen samun nasararsu.
“Amma muna kira ga INEC da ka da ta bayar da kai bori ya hau a matsayinta na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa tare da kare mutuncnta ta hanyar kin yin abin da ya saba wa doka.
“Muna tunatar da hukumar INEC cewa ‘yan Nijeriya suna sa ido sosai kan yadda za ta magance wannan batun na TNN, kuma duk abin da za ta yi zai tantance ko ‘yan Nijeriya za su iya dogaro da ita don shirya sahihin zabbe mai cike da adalci a 2027,” in ji sanarwar.
Ya kuma ce, “Idan aka yi la’akari da siyasar da ta riga ta wuce gona da iri gabanin zaben 2027, mun yi imanin INEC ba za ta yi wani abu da zai kara ta’azzara lamarin ba”.
Ya bukaci INEC da ta bi ka’idojinta da kuma kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya, wanda hakan zai ba da damar kungiyarsa ta yi rajista a matsayin jam’iyyar siyasa daidai da dokokin kasar da kuma yin takara a dukkan matakai daga kananan hukumomi a babban zabe mai zuwa.
A halin da ake ciki, TNN ta yi kira ga dukkan magoya bayanta su kwantar da hankulansu kan batun yin rajista.
“Mun san cewa da yawa daga cikin magoya bayanmu masu yawa sun fusata da rahoton matsin lambar da ake yi wa INEC kan wannan batun. Amma dole ne su ci gaba da bin doka da oda yayin da muke jiran hukuncin INEC.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp