Hukumar kula da kafafen yaɗa labarai ta Nijeriya (NBC), ta soke lasisi kafafen yaɗa labarai guda 52 a fadin kasar kan karya dokoki da ka’idojin hukumar.
Hukumar na bin tashoshin bashin naira biliyan N2.6 tun 2015.
- CDD Ta Soki NBC Kan Cin Tarar Trust TV Da Wasu Miliyan 20
- NBC Ta Ci Tarar Trust TV Tarar Miliyan 5 Kan Yada Ayyukan ‘Yan Bindiga
Tashoshin da aka rufe din sun hada da gidan talabijin mai zaman kansa na African Independent Television (AIT), Raypower FM; Silverbird Television da wasu kafafe 49 a sassan kasar nan.
Darakta-janar na hukumar NBC, Malam Balarabe Shehu Ilelah, shi ne ya sanar da hakan lokacin ganawarsa da ‘yan jarida a Abuja ranar Juma’a.
Shehu ya ce, gargame kafafen bai da alaka da wata siyasa kwata-kwata illa domin a tabbatar da bin dokoki da ka’idojin hukumar.
Ilelah ya bukaci tashoshin da su gaggauta biyan kudaden da ake binsu cikin awa 24 domin kauce wa yanke alakata ta gaba daya.