Matatar Man Fetur ta Dangote ta sake rage ₦10 akan farashin man fetur, inda ta rage daga N835 a hukumance zuwa ₦825 kan kowace lita.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, wasu majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin sun bayyana a ranar Litinin cewa, tun da farko, ‘yan kasuwar sun biya Matatar Naira 835 kan kowacce lita amma daga baya, sai aka mayar musu da ragin Naira 10 bayan sun yi dakon man daga matatar.
Wata majiya ta tabbatar da cewa “Matatar man Dangote ta fara bayar da rangwame kan kayayyakin da take samarwa, babu sanarwa a hukumance, amma an tura wa ‘yan kasuwar da rangwamen a asusun su bayan sun fitar da man daga Matatar.”
Wannan rangwamen farashin duk da cewa ba a hukumance yake ba, amma ya bai wa kwastomomin Dangote damar siyar da mai akan farashi mai rahusa a tsakanin ₦830 zuwa ₦835 kan kowacce lita.
Wannan nasarar ta zo ne makonni kadan bayan da matatar ta yi ragin farashi sau biyu a jere a cikin mako guda a cikin watan Afrilu, inda ta rage farashin man ta daga ₦880 zuwa ₦835 kan kowace lita.
Ana kyautata zaton cewa, ragin na da nasaba da sabunta tsarin sayen danyen mai da takardar Naira, biyo bayan dakatarwar da aka yi na wucin gadi.
Kokarin samun wata sanarwa a hukumance daga Kakakin Rukunin Dangote, Anthony Chiejina, kan batun rangwamen ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp