Ministar kudi da kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arzikin kasa, Hajiya Zainab Ahmad, a ranar Alhamis ta shaida cewar, Gwamnatin tarayyar Nijeriya na kashe zunzuturun kudi da yawansu ya kai naira biliyan N18.397 a bangaren tallafin Mai a kullum.
Sannan, ministar ta ce, adadin naira tiriliyan N6.210 ne ake biya a matsayin tallafin Mai ga ‘yan kasuwa masu zaman kansu daga shekarar 2013 zuwa 2022.
- Buhari Ya Bude Rukunin Gidajen Da Gwamna Zulum Ya Gina Wa Malamai A Jihar Borno
- Buhari Ya Sake Nada Bashir Ahmad, Ya Kara Masa Girma Zuwa Mataimaki Na Musamman
Ministar ta ce, gwamanti ba za ta ci gaba da narka irin wannan maguden kudaden wajen biyan tallafin Mai ba, ta kara da cewa akwai shawarar da masu ruwa da tsaki suka bayar ciki har da Majalisar wakilai ta kasa da jam’iyyun siyasa na a tsaida biyan tallafin ko a ci gaba da biya.
Zainab Ahmad ta yi wannan bayanin ne a lokacin da ta bayyana a gaban kwamitin bincike na Majalisar wakilai ta tarayya da aka daura wa alhakin binciken tallafin Mai da aka narka daga 2013 zuwa 2022 wanda Hon. Ibrahim Aliyu ke jagorantar kwamitin.
Ta kara da cewa, ma’aikatarta ta biya naira Tiriliyan N1.774 daga 2013 zuwa 2016 yayin da sauran kuma aka samu daga karkashin shirin PMS under-recovery na kamfanin Mai na kasa (NNPC).
Ta yi bayanin cewa Gwamnatin tarayya na biyan tallafin Mai har naira Biliyan N18.397 kowace rana.
Ministar ta kara da cewa, tsarin kashe kudi na (MTEF) tuni aka aike wa Majalisar Dokoki ta kasa, inda gwamanti ta yi harsashen kashe tiriliyan N3.35 a cikin rabin shekara.