Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis ya kai ziyara Maiduguri tare da kaddamar da wani sabbin rukunin gidajen da Gwamna Babagana Umara Zulum ya gina wa malamai a jihar.
Rukunin gidajen na daya daga cikin manyan ayyuka 600 wadanda Zulum ya aiwatar, an gina rukunin gidajen a yankin Bulumkutu, kan titin filin jirgi.
- Tubabbun ‘Yan Boko Haram Sun Gudanar Da Aikin Tsabtace Muhalli A Maiduguri
- Dan Sanda Ya Mutu A Harin Da ISWAP Ta Kai Hanyar Maiduguri-Damaturu
Baya ga wannan, Gwamna Zulum ya gina karin wasu gidajen a cikin makarantun sakandire da firamari domin malamai a fadin jihar.
Shugaban kasa ya isa a rukunin gidajen da misalin karfe 12 na rana tare da Gwamna Zulum da Mataimakinsa, Umar Usman Kadafur da Mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima, tare da jiga-jigan gwamnatin tarayya dake yankin Arewa Maso Gabas.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp