Masarautar Zazzau ta tabbatar da rasuwar Alhaji Ramalan Yero, mahaifin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Dokta Muktar Ramalan Yero.
Sanarwar da ta fito daga bakin Sarkin Fadan Zazzau, Alhaji Abbas Ahmed Fatika, inda ya ce marigayin ya rasu da yammacin ranar Litinin bayan fama da rashin lafiya.
- NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APC
- NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APC
Tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar s unguwar Kaura da ke cikin birnin Zariya, a Jihar Kaduna.
Masarautar ta aike da ta’aziyyarta ga iyalan mamacin da É—aukacin al’ummar Jihar Kaduna bisa wannan rashi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp