Wasu Ma’aikatan Hukumar Ilimi na ƙaramar hukumar Damboa (LEA) guda biyu sun rasa rayukansu a ranar Litinin, sakamakon fashewar bam a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri da ke Jihar Borno.
Waɗanda suka rasu sun haɗa da Blessing Luka da Gideon Bitterleaf, kuma suna cikin tafiya daga Damboa zuwa Maiduguri lokacin da lamarin ya faru.
Shaidu sun ce waɗanda abin ya rutsa da su na zaune a gaban wata motar Toyota Hiace da ke ɗauke da mangwaro, lokacin da motar ta taka wani bam da ake zargin ‘yan tada ƙayar baya ne suka birne a ƙarƙashin ƙasa.
Fashewar bam ɗin ta kashe su nan take, inda wasu da ke cikin motar suka samu raunuka.
Wani ma’aikaci a ƙaramar hukumar Damboa ya tabbatar da sunayensu, inda ya bayyana su a matsayin ƙwararru masu jajircewa a ɓangare aikinsu na harkar ilimi.
Jami’an tsaro sun killace wajen da lamarin ya faru, kuma suna ci gaba da bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp