Babu wata ’yantacciyar kasa da za ta hakura da muradunta domin wata ta biya bukatunta na son rai. Yayin da Amurka ta yi gaban kanta wajen kakabawa kasashe haraje-harajen kwastam na babu gaira ba dalili, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kin amincewa da salon cin zali, inda ta sha nanata cewa, sai ta ga abun da ya ture wa buzu nadi, a yakin cinikayya da Amurkar ta tayar. Lallai tsayuwar kasar Sin ya ba kasashe masu tasowa kwarin gwiwa, kuma ya nuna cewa, lokaci ya wuce da za a rika yi wa ’yantattun kasashe danniya da cin zali domin biyan bukatu na kashin kai.
Hakika kasar Sin ta gina tubali mai karfi da ta dora tattalin arzikinta a kai, tare da mayar da hankali wajen habaka bukatu na cikin gida ta yadda ta kaucewa dogaro da kasashen waje, yayin neman ci gaba. Don haka duk wani matsi na Amurka, sai ya fi tasiri kanta maimakon kasar Sin. A ganina, wannan dalili ne ya sa Amurka neman sulhu ta hanyar neman tattaunawa da kasar Sin. Za mu iya cewa, ana maraba da tattaunawar duk da dama can Sin ta sha cewa, yaki ba zai samar da mafita ba, kuma kofarta a bude take a tattauna bisa adalci da sanin ya kamata.
- Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil
- Jami’ar Maryam Abacha Ta Rufe Ɗakunan Kwanan Ɗalibai Saboda Aikata Rashin Ɗa’a A Kano
Bisa la’akari da karfinsu na tattalin arziki, Sin da Amurka na taka muhimmiyar rawa ga tattalin arzikin duniya da ma harkokin kasuwanci da cinikayya tsakanin kasa da kasa. Kuma tattaunawa ta baya bayan nan da kasashen biyu suka yi za ta taka rawa gaya wajen rage sabanin dake tsakaninsu da aza tubalin zurfafa hadin gwiwa.
Hakika yadda Sin ta tsaya kai da fata, ita ce kadai hanya ta nuna wa Amurka cewa fin karfi ba zai haifar da da mai ido ba, kuma tabbas hakan ya kwatar wa kasashen duniya musamman masu tasowa ’yanci, tare da ba su kwarin gwiwar bijirewa cin zali. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp