A yau Talata 13 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya soki kasar Amurka a wani taron manema labarai, kan yadda ta yi watsi da kyakkyawan fatan kasar Sin, da kuma kakaba “harajin fentanyl” a kan kasar Sin ba bisa ka’ida ba.
Ya kara da cewa, wannan mataki ya yi mummunan tasiri sosai ga tattaunawa da hadin gwiwar Sin da Amurka a fannin yaki da muggan kwayoyi da kuma kawo cikas ga muradun kasar Sin.
- China Da Amurka Sun Yarda Da Rage Harajin Kayayyakinsu Domin Sasanta Rikicin Kasuwanci
- Mahaifin Tsohon Gwamnan Kaduna, Ramalan Yero, Ya Rasu
Wani sakamakon binciken jin ra’ayoyi ta shafin intanet da kafar yada labarai ta CGTN ta fitar ya nuna cewa, kashi 91.8 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyi sun yi imanin cewa, matakin na Amurka ba komai ba ne illa fakewa da guzuma don a harbi karsana ta fuskar siyasa da cin zarafi ta hanyar amfani da haraji, da nufin boye gazawarta a fannin shawo kan muggan kwayoyi. Ana kuma daukar lamarin da aka kira da “harajin fentanyl” a matsayin mai matukar illata tsarin kasuwancin kasa da kasa.
Lin Jian ya bayyana cewa sha’anin kwayoyin fentanyl batu ne na Amurka, ba na kasar Sin ba, kuma alhakin abin ya rataya ne a wuyan Amurka.
A cewar bayanan da suka fito daga Cibiyar Rigakafi da Shawo Kan Annobar Cututtuka ta Amurka (CDC), a tsakanin kusan Amurkawa miliyan 280 masu shekaru 12 zuwa sama, akalla ana samun mutum daya cikin ko wadanne mutane 12 da ke amfani da muggan kwayoyin. Kana kimanin kashi 60 cikin 100 na yawan muggan kwayoyin da ake sarrafawa a duniya Amurka ake kaiwa.
A cikin binciken jin ra’ayoyin, kashi 91 cikin 100 na masu bayyana ra’ayoyi, sun yi imanin cewa shaye-shayen miyagun kwayoyi na daga cikin manyan abubuwan da ke barazana ga rayuwar Amurkawa.
An wallafa sakamakon binciken a dandalolin CGTN a cikin harsuna biyar da suka hada da Ingilishi, Sifaniyanci, Faransanci, Larabci, da Rashanci. A tsakanin sa’o’i 24 da kaddamar da binciken, masu amfani da intanet fiye da 12,000 ne suka shiga cikin binciken tare da bayyana ra’ayoyinsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp