Kusan a duk shekara, batun fuskantar kalubalen da manoman kasar nan ke fuskanta, sai kara zama jiki yake yi.
Wannan na faruwa ne, duk da namijin kokarin da manoman kasar ke ci gaba da yi, na samar da wadataccen abinci.
Wasu daga cikin manyan kalubalen da manoman ke ci gaba da fuskanta sun hada da, kalubalen rashin tsaro, gazawar Gwamnatin Tarayya da ta jihohi na cikawa manoman alkawuran da suka dauka za su yi manoman.
- Nijeriya Ta Biya Bashin Ɗaliban Da Ke Karatu A Ƙasashen Waje
- Noman 2025: Dole Ne Manoma Su Kiyaye Hasashen Hukumar NiMet
Kazalika, wannan rashin cika alkawuran na ‘ya’yansa masu rike da madafun iko a kasar, ya sanya wa, akasarin manoman kasar fitar da rai.
Wasu daga cikin rashin cika alkawuran, su ne, rashin rabar masu da kayan aikin noma, akan farashi mai sauki, kamar su Taraktocin noma ba su rancen kudin yin noma, wanda hakan ke janyowa ayyukansu na yin noma nakasu, musamman kan yadda ba su iya noma amfani da yawa, yin girbi maras kyau da kuma yin asara, a lokacin girbi.
Mun bijoro da wannan batun kalubalen da manoman ke ci gaba da fuskanta ne, musamman duba da cewa, kakar noman bana, ta karato, musamman ganin cewa, an fara samun saukar Ruwan sama, a wasu sassan kasar nan, inda kuma tuni, mahara suka mamaye wasu yankunan kasar da ake yin noma.
Akasarin fadin kasar nan, musamman a yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma duba da cewa, wadannan yankunan biyu, sun yi fice wajen yin noma, amma abin takaici, ‘yan bindiga daji, ‘yan ta’adda da kuma wasu Fulani Makiyaya, sun mayar da wadannan yankunan fagen daga, inda suka kashe manoma da kuma lalata amfanin gonakansu.
Bugu da kari, wadannan bata garin sun kuma kone wasu gidajen alumomin da ke a wadannan yankunan, wanda hakan ya janyo tarwatsa su, daga matsugunna su, inda kuma suka kwace yankunan.
Hakazalika, a wasu guraren, wadannan bata garin, har ma haraji da biyan wasu kudade suke kakabawa manoma kafin su bar su, noma gonakansu ko kuma su girbe amfanin gonakansu.
Wannan matsalar ta sanya yin noma, ya fita daga ran wasu manoma da dama, wanda illar hakan, ke janyo yunwa, talauci, rashin abinci mai gina jiki a kasar.
Misali, wani rahoton hadadin guiwa a tsakanin Gwamnatin Tarayayya da Gwamnatocin jihohi tare da goyon bayan Hukumar Samar da Abinci FAO da kuma sauran wasu masu hadaka, da aka fitar a kwanan baya ya nuna cewa, ana hasashen ‘yan Nijeriya miliyan 30.6, musamman a jihohi 26, ciki har da Abuja, ciki har da wadanda ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira su 150,978 za su fuskanci matsalar karancin abinci daga watannin Yuni zuwa na Agustan 2025.
Kazalika, wannan rahoton ya kula da cewa, duk da samun raguwar kayan abinci da kuma raguwar farashinsa a daukacin fadin Nijeriya, an kiyasata cewa, ‘yan kasar miliyan 24.9 cikinsu har da wadanda ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira a jihohi 26 ciki har da Abuja su 116,765, a yanzu haka, suna ci gaba da fuskantar karancin abinci, wanda hakan zai kara munana a cikin watan Mayun 2025.
Wata karin matsalar ita ce, hasashen kwanan baya da Bankin Duniya ya yi, na samun karuwar yunwa da fatara a 2027.
Wannan hasashen na Banki, na da nasaba da yadda Gwamnati ta yi watsi da bai wa fannin noma daukin da ya kamata, musamman, ga manona.
A saboda wadannan matsalolin da muka zayyano ne, mu a matsayin mu a wannan Jaridar, muke kalubalantar mahukuntan kasar kan cewa, ya zama wajbi su rungimi tsare-tsaren da za su warware wa manoman kasar, matsalolin da suke ci gaba da fuskanta, musaman kalubalen rashin tsaro da samar masu da kayan aikin gona a kan lokaci.
Muna kuma kalubalantar Gwamnatin da cewar, ba wai kawai ta buge da bayar da tabbaci kawai ba, amma ta dauki matakan da suka kamata, musamman domin ta tsamo manoman kasar, daga cikin kalubalen da suke ci gaba da fuskanta, domin su samu sukunin ci gaba da yin sana’arsu, ta noma.
Kazalika, muna kira ga Gwamnatin da ta samar da matakan da suka dace, na tattabar da tsaro, musamman a yankunan da ake yin noma, ta hanyar tura jami’an tsaro, da za su rinka bai wa gonakan manoma da su kansu manoman kariya daga hare-haren ‘yan bindiga daje ta kuma kafa shirye-shiyen yin aiki da ‘yansanda alumma tare da kuma samar da wata dama ta tattaunawa da shugabannin alumomi, domin lalubo da mafta kan dukka wata matsala da kunno kai a cikin alumma.
Ya zama wajbi Gwamnati ta rinka rabar da kayan aikin noma ga matasa a kan lokaci, kamar Takin zamani, ingantaccen Irin noma, magugunan feshi da sauransu.
A nan, muna bayar da shawarar cewa, ya zama wajbi, a rungumi irin tsarin da Gwamnatin jihar Jigawa ta fito da shi, nan a kafa Cibiyoyin rabar da kayan aikin noma guda 30, inda ta rabar da sama da kayan aikin noman rani na Shinkafa 54,000 kan farashin kaso 30.
Domin a dakile matsalar ‘yan kasuwa masu sayen amfanin gona kai tsaye daga gun manoma domin boyewa, muna kira ga Gwamnati da ta tura kayan aikin noma kai tsaye, zuwa kungiyoyin manoma wanda hakan zai bai wa manoman saukin samun rancen kudaden yin noma, samun horo da kuma samun dabarun yin noma na zamani
Ya kuma zama wajibi, Gwamnati ta samar da ababen more rayuwa a karkara, kamar inganta hanyoyin da ke a cikin karkara, samar da runbunan adama amfanin gona, rage asarar da manoma key i, in sun yi girbi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp