Idan kin gama haila, akwai wasu abubuwa da za ki yi don tsafta da tsarkaka:
- Yin Wankan Tsarki (Ghusl)
Bayan kin gama haila, dole ne ki yi wankan tsarki kafin ki dawo ibada kamar Sallah da Azumi. Ga yadda ake yi:
Ki fara da niyya a zuciyarki. Ki wanke hannayenki sau uku. Ki wanke gabanki da ruwa mai tsarki mai tsarkakewa wanda kalarsa bar a canja ba ko dandanonsa ko kamshinsa, amma ba a sanya sabulu.
Sannan za ki yi alwala kamar yadda ake alwalar Sallah, amma ban da kafafu iya shafar kai kawai. Ki wanke kanki da ruwa sau uku har ruwa ya isa fatar kanki. Ki wanke jikinki gaba daya, kuma a rika wankewa da kyau, ki fara daga bangaren dama ki zo hagu, daga karshe sai ki wanke kafafunki kamar yadda kike a alwala, idan aka yi haka wanka ya kammala. Kuma wannan alwalar da kika yi ta wannan wankan za ki iya yin Sallah da ita in dai baki shafi cikin al’aurarki ba.
- Ya Kamata A Kori Ministan Ilimi – Aisha Yesufu
- Ƙungiyar Fulani Makiyaya Ta Nuna Damuwarta Na Ɓacewar Mataimakin Shugabanta
- Amfani da Miski
Bayan wanka, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ba da shawarar mace ta yi amfani da miski domin tsarkake jikinta da kuma rage warin haila.
Ga yadda ake yi:
Ki jika auduga da miski mai kamshi. Ki shafa a wurin da jinin haila ya tsaya don tsafta da jin kamshi.
- Sauya Tufafi da Shirya Sabuwar Tsabta
Ki tabbatar kin canza tufafin da kika sa lokacin haila. Ki yi amfani da sabbin kayan ciki don jin tsabta.
- Komawa Ibadah
Bayan wankan tsarki, za ki iya komawa yin Sallah, azumi, da sauran ibadu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp