ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

by Rabi'u Ali Indabawa
7 months ago
Amurka

A Wani lamari mai kama da tatsuniya ko wasan kwaikwayo! Ta yaya za a ce masana’antar shirya Fina-finai ta Amurka (Hollywood) ta fara durkushewa, ta kama hanyar zama tarihi!

Dangane da kiyasin shafin intanet na the-numbers.com, ya nuna Amurka na samar da fina-finai kusan 26,000 kowace shekara; kasar da ke binta a baya, tana fitar da kusan 5,000. Bugu da kari, hada-hadar kudi na fina-finan da aka yi a Amurka ya kai Dala biliyan 650 a cikin shekara daya. Kasa ta biyu a wannan jerin, tana da kusan Dala biliyan 60 a shekara.

  • Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Ta Daina Kassara Kamfanonin Fasaha Da Na AI Na Sin
  • Kasashe 10 Da Suka Fi Tsananin Zafi A Duniya A Bana

A ranar Lahadin da ta gaba ne, Shugaban Amurka, Donald Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na sada zumunta, shugaban ya yi ikirarin cewa, masana’antar fina-finan Amurka “kimarta na durkushewa cikin sauri” kuma fitattun wurare da yawa a duk fadin kasar “Suna cikin mawuyacin hali” saboda fina-finan da ake shiryawa a kasashen waje suna da rangwamen farashi.

ADVERTISEMENT

Saboda haka, ya ba da izini ga Ma’aikatar Kasuwanci da Wakilin Kasuwancin Amurka su kakaba harajin kashi 100 bisa 100 a kan duk wani fim da aka shigo da shi cikin Amurka da wanda ake shiryawa a kasashen waje.

Wannan mataki ya haifar da gagarumar muhawara a duniya. Yayin da manufar ke da nufin farfado da Hollywood da karfafa shirya fina-finai na cikin gida.

LABARAI MASU NASABA

EU Ta Koka Da Yadda Yaduwar Ta’addanci A Sahel Ke Barazana Ga Tsaron Turai

Trump Ya Caccaki Kasashen Turai Bayan Ayyana Nahiyar A Matsayin Mai Rauni

Amma mu tambayi kanmu, shin da gaske wannan ita ce hakikanin manufar?

Amma bari mu yi la’akari da wannan hasashen mu gani, ko shi ne ya fusata Amurka ta maka harajin kashi 100 bisa 100 kan fina-finai da ake shigar da su daga kasashen waje ko kuma wadanda aka shirya a ketare?

Akwai wani kirkirarren fim mai suna ‘Ne Zha 2’ da masana’antar shirya fina-finai ta kasar Sin ta shirya a baya-bayan nan. Kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayar da rahoton cewa, wannan fim ya zama na farko da ya samar da Dala biliyan 1 a kudin tikitin shiga a kasuwar cikin gida kadai. Bugu da kari, wannan adadi, ya haura sama da Dala biliyan 2 a kudaden shiga a duk duniya. Wannan abin a yaba ne, amma a wani bangare,

Wannan rahoton kadai, zai iya fusata gwamnatin Amurka, ganin cewa, kasar tuni ta yi wa kasar Sin bakin fenti da cewa, ita ce babbar abokiyar hamayyarta a bangaren kasuwanci a duniya.

In ba a manta ba, da ma tun bayan rantsar da gwamnatin Trump, ya sha alwashin kakaba haraji kan duk hajojin da ake shigowa da su Amurka. Hukuncin da gwamnatin ta yanke, lallai ba shakka ba ta canja ra’ayi ba kamar yadda ta yi da sauran sanarwar haraji, wanda hakan ya tabbatar da cewa, yakin cinikayyar duniya har da fina-finai.

Tun ba a yi nisa ba, Amurkawa sun fara dandana kudar yakin cinikayya, inda farashin kayayyaki suka fara tsauri ga ‘yan kasar.

Don haka, akwai yiwuwar Amurkawa za su nisanta daga duk wani fim da aka shirya a ketare da zarar sun ga farashin tikitin ya yi tsada. Shin hakan zai iya zama abin da gwamnatin ke so?

Irin wannan hukunci da Amurka ke dauka, hakan yana da mummunan tasiri akan ‘yan kasarta ko da kuwa lamarin zai shafi sauran ‘yan kasashen waje.

Wai mu tambayi kanmu mana, Amurka ta rasa Dattawa da Masana ne wanda za su ba ta shawara kan harkokin tattalin arziki ne, ko kuwa Gwamnatin ta yi kunnen uwar shegu da shawarwarin su ne?

Masana da dama na ganin cewa, wannan mataki na zabga harajin kashi 100 bisa 100 a fina-finai zai haifar da mummunan sakamako ga masana’antar Hollywood, sannan kuma zai gurgunta kyakkyawar alakarta da takwarorinta na duniya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

EU Ta Koka Da Yadda Yaduwar Ta’addanci A Sahel Ke Barazana Ga Tsaron Turai
Kasashen Ketare

EU Ta Koka Da Yadda Yaduwar Ta’addanci A Sahel Ke Barazana Ga Tsaron Turai

December 14, 2025
Trump Ya Caccaki Kasashen Turai Bayan Ayyana Nahiyar A Matsayin Mai Rauni
Kasashen Ketare

Trump Ya Caccaki Kasashen Turai Bayan Ayyana Nahiyar A Matsayin Mai Rauni

December 14, 2025
Rwanda Ta Musanta Hannu A Rikicin Da Ya Barke A Kibu Da DR Congo
Kasashen Ketare

Rwanda Ta Musanta Hannu A Rikicin Da Ya Barke A Kibu Da DR Congo

December 14, 2025
Next Post
Crystal Palace Ta Lashe Kofin FA Karon Farko, Ta Doke Manchester City 1-0

Crystal Palace Ta Lashe Kofin FA Karon Farko, Ta Doke Manchester City 1-0

LABARAI MASU NASABA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.