Hukumar ‘Yan Nijeriya Mazauna Ƙasashen Ƙetare (NiDCOM), ta karɓi ‘yan Nijeriya 13 da aka yi safararsu zuwa ƙasashen Ghana da Mali, waɗanda suka haɗa da ‘yan mata 12 da ƙaramin yaro ɗan shekara biyar.
A cewar wata sanarwa daga shugaban sashen yaɗa labarai na NiDCOM, Abdur-Rahman Balogun, shugabar hukumar, Abike Dabiri-Erewa, ce ta karɓi waɗanda aka ceto.
- Kasar Sin Na Adawa Da Kai Wa Fararen Hula Da Kayayyakin More Rayuwa Hari A Sudan
- Yankin Taiwan Ba Shi Da Iko Ko Hujjar Halartar Taron WHA
‘Yan matan sun bayyana cewa an yaudare su da alƙawarin sama musu aikin yi, amma daga baya aka tilasta musu yin karuwanci a Ghana da Mali.
Sun kuma bayyana cewa sun fuskanci cin zarafi, duka, da azaba daga hannun waɗanda suka yi safararsu.
Abike Dabiri-Erewa ta ba su tabbacin cewa NiDCOM za ta ci gaba da tallafa musu da hanyoyin komawa gida lafiya, tare da haɗin gwiwa da gwamnonin jihohinsu domin samun cikakken taimako.
Ta kuma yi kira da a cafke masu safarar mutane tare da fallasa sunayensu bayan an gurfanar da su a gaban kotu, domin daƙile laifi.
NiDCOM ta miƙa waɗanda aka ceto ga hukumar NAPTIP domin tantance su da kuma ci gaba da ba su kulawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp