Wata kotu a Kano ta yanke wa mutum biyar hukuncin ɗaurin wata ɗaya a gidan yari ko kuma su biya tara Naira 25,000 kowannensu, saboda awakin da suka ke kiwo sun ci shukar gwamnati a titin Lodge Road da Race Course Road a cikin birnin Kano.
Bayan haka, kotun ta umarce su da su biya Naira 100,000 a matsayin tara saboda ɓarnar da awakin suka yi.
- ‘Yansanda Sun Tarwatsa Wuraren Haɗa Jabun Taki A Bauchi, An Cafke Mutum 5
- Shirye-shiryen Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Minista
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa Ma’aikatar Muhalli ce ta kai ƙarar, domin kare kayan gwamnati da kuma tsaftar muhalli.
Lauyar gwamnati, Barista Bahijjah H. Aliyu, ta ce waɗanda ake tuhuma sun karya dokar Lafiyar Jama’a ta 2019, wadda ta haramta barin dabbobi su lalata dukiyar gwamnati ko muhalli.
Gwamnati ta ce shukar da awakin suka lalata na cikin wani shiri da ake yi don ƙawata birnin Kano da kuma inganta lafiyar iskar da jama’a ke numfashi da ita.
Kotun ta bayyana cewa mutanen sun aikata laifin sakaci da kuma jawo asarar dukiyar jama’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp