Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce sai an samu zaman lafiya da tsaro kafin masu saka da ci gaban tattalin arziƙi su tabbata.
Ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin taron tarbar masu zuba jari na ƙasa da ƙasa da ake kira “Taravest” da aka gudanar a birnin Jalingo, babban birnin Jihar Taraba.
- ‘Yansanda Sun Tarwatsa Wuraren Haɗa Jabun Taki A Bauchi, An Cafke Mutum 5
- Kotu Ta Soke Umarnin Kwace Filin Asibitin Tiamin, Ta Umarci Gwamnatin Kano Ta Biya Diyyar ₦2.6bn
Atiku, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, ya ce Jihar Taraba na da ɗimbin damar tattalin arziƙi, musamman a fannoni kamar noma, ma’adinai da yawon shaƙatawa.
Amma sai an samar da tsaro da kwanciyar hankali kafin a iya cin moriyar waɗannan damarmaki.
Ya shawarci gwamnati da ta rage haɗuran da ke hana masu saka jari shigowa ta hanyar kawo ƙarshen cikas da kawo sauƙaƙa matakai na zuba jari.
“Zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a cikin al’umma na da matuƙar tasiri wajen jan hankalin masu zuba jari,” in ji Atiku.
Ya ƙara da cewa ya zama dole gwamnati ta fito da tsare-tsare masu ma’ana da kuma manufofi masu ƙayatarwa don jawo masu zuba jari.
Atiku ya kuma ce ƙarfafa hukumomi da inganta ababen more rayuwa na da muhimmanci matuƙa domin su ne ginshiƙan ci gaba mai ɗorewa.
Ya bayyana cewa babu wata jiha a Nijeriya da za ta iya ci gaba da kanta ba tare da haɗin gwiwa ba.
Don haka ya ce dole ne a kafa ƙawance mai ƙarfi tsakanin gwamnati, masu zuba jari, ‘yan kasuwa da al’umma domin cike giɓi da buɗe ƙofofin ci gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp