Gwamnatin Tarayya ta zuba jarin Naira tiriliyan 1.5 domin magance matsalar abinci da sauran ƙalubalen tattalin arziƙi, in ji Ministan labarai da yaɗa manufofin ƙasa, Mohammed Idris. Ya bayyana wannan fata ne yayin jawabi a taron ƙoli na ƙungiyar Masu hulɗa da jama’a ta Nijeriya (NIPR) da aka gudanar a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom.
Ministan ya ce Ajandar Fatan Sabon Sauyi (Renewed Hope Agenda) ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu na da nufin fitar da Nijeriya daga matsalolin da take fuskanta.
- Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa
- Shirye-shiryen Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Minista
Idris ya jaddada cewa shekaru biyu na gwamnatin Tinubu sun nuna ci gaba mai ma’ana, musamman ta hanyar ware kuɗaɗen farfado da Bankin Noma da suka kai Naira tiriliyan 1.5. Ya kuma yi kira ga masu aikin hulɗa da jama’a da su rungumi wannan sauyi domin taimakawa wajen inganta sunan Nijeriya da jawo hankalin masu zuba jari a fannin tattalin arziƙi.
Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Pastor Umo Eno, ya samu wakilci daga mataimakiyar gwamna Dr. Akon Eyakenyi, inda ta yi bayani kan rawar da masu hulda da jama’a ke takawa wajen bunkasa tattalin arziki. Ta bayyana cewa masu hulda da jama’a za su iya yin aiki tare da kafafen yada labarai domin tallata sunan Nijeriya a duniya.
Shugaban NIPR, Dr. Ike Neliaku, ya yi nuni da babban gibin da ake samu a fannin sadarwa tsakanin shugabanni a matakai daban-daban, inda ya ce wannan rashin sadarwa tana kawo cikas wajen samun ci gaba. Ya yi kira da a inganta sadarwa a bagarorin shugabanci domin samun ci gaba a Nijeriya da bunkasar tattalin arziki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp