• English
  • Business News
Sunday, August 31, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (2)

by Mairo Muhammad Mudi
3 months ago
in Bakon Marubuci
0
SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (2)
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Lokacin da gwamnatin tarayya ta kafa babban birnin tarayya (FCT) da Hukumar Raya FCT (FCDA) a shekarar 1976, babu wata muhimmiyar cibiyar more rayuwa a cikin kowane gari na FCT; kamar makarantu, asibitoci, ruwan sha, layin waya, ofishin posta, wutar lantarki da sauran makamantansu. Don haka ne, aka kafa sansani ‘Field Base FCDA’ a Suleja. Haka kuma, an yi amfani da jami’an karamar hukumar, domin tallafa wa sabuwar hukumar FCDA ta tsaya da kafarta.

Malam Abdullahi Ladan ne aka dora wa nauyin rike mukamai biyu a lokaci guda, Sakataren Karamar Hukumar Abuja, kamar yadda ake kiransa a wancan lokaci, sannan kuma shi ne shugaban lissafi na farko na FCDA tun a shekarar 1976, kafin a kafa tsarin gudanarwar hukumar. Yanzu haka, shi ne Wazirin Zazzau na Suleja, yana kuma da shekaru 96, yanzu haka kuma yana kwance sakamakon rashin lafiya. Babban abin takaici shi ne, an manta da dukkanin irin gudummawar da ya bayar tun kafin ya bar duniya.

  • Za Mu Riƙe Wa Minista Tijjani Muƙaminsa Bayan Hamɓarar Da Tinubu A 2027 – El-Rufai 
  • Ingancin Tattalin Arzikin Sin Mai Bude Kofa Na Bayyana Sosai Duba Da Yawan Zuwan Baki Masu Sayayya

Ofisoshin Sakataren Gudanarwa na farko da na biyu na FCDA da na Ministan FCT na farko, duk suna Suleja ne. A watan Yuni na 1977, FCDA ta ba da kwangilar tsara tsarin babban birnin Abuja ga kamfanin ‘International Planning Associates’ (IPA).

IPA ta kammala aikin tare da mika shi ga Sakataren Gudanarwa na FCDA, Marigayi Abubakar Koko, a ranar 15 ga Fabrairun 1979. A wannan lokaci ne kuma, gwamnatin tarayya ta nemi a sauya sunan garin Abuja, domin amfani da shi a matsayin sabon babban birnin tarayya, inda Masarautar ta amince ba tare da neman wani diyya ba.

Saboda haka, ya zama dole ga IPA ta rubuta wani karin bayani a shafin farko na tsarin Birnin Abuja cewa: “IPA ta samu sanarwa bayan buga wannan rahoto cewa; za a sauya sunan garin Abuja da ke Jihar Neja zuwa Suleja, don gujewa rudani da sabon sunan Babban Birnin Tarayya. Duk inda aka ambaci Abuja a cikin wannan rahoto, yana nufin tsohon garin Abuja.”

Labarai Masu Nasaba

Ranar Hausa: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

Yaushe Shugaban Kasa Zai Ba ‘Yan Matan Yobe Nasu Kyaututtukan

A gefe guda kuma, al’ummar yankin ne suka sadaukar da gonakinsu, domin amfanin jama’a wajen gina sansanin FCDA. An cimma yarjejeniya cewa; a karshen amfani da filin, za a mayar da shi ga al’umma. Malam Ladan, ya dage har aka tabbatar da wannan yarjejeniya a rubuce kuma Marigayi Abubakar Koko, Sakataren FCDA, ya sa hannu don kada a samu sabanin tarihi.

Amma duk da haka, ba a mika kadarar ba har zuwa shekarar 1987, bayan fafutukar kwato ta tsawon lokaci. Daga bisani kuma, aka mika ta ga kungiyar tsoffin sojoji ta Nijeriya (Nigerian Legion), bayan sun nemi haka. Abin bakin ciki, gwamnatin tarayya ta kara lissafa filin a matsayin daya daga cikin kadarorinta da za a sayar a zamanin mulkin Obasanjo.

Da ba a gano takardun da Marigayi Koko ya sa hannu a kansu daga cikin tsohuwar ajiyar Jihar Neja ba, da an kwace filin. Wannan kuwa sakamakon hangen nesa ne na Malam Ladan.

Bayan dawo da ikon filin a karo na biyu a ranar 30 ga Oktoba, 2007, al’umma suka mika filin ga Gwamnatin Jihar Neja, domin bai wa Jami’ar IBB ta jihar damar kafa reshe a Suleja. Amma fiye da shekara 17 da yin haka, Gwamnatin Neja ta kasa ware ko sisin kwabo don fara gina wannan reshe.

Abin takaici, tun bayan kirkiro Jihar Neja a 1975, babu wata jami’ar gaba da sakandire da gwamnatin jiha ko ta tarayya ta kafa a Masarautar Suleja, duk da koke-koke da dama, har ma da kiran da dan Majalisar Suleja ya yi kwanan nan a gaban majalisar jihar. Wasu sassan na jihar har suna alfahari da dama daga cikin irin wadannan cibiyoyi. Har da shirin kafa makarantar koyon aikin jinya a tsohon wurin makarantar jinya ta FCT a sansanin FCDA ya zama kawai na cin fuska ne kawai. Hakan na faruwa duk da cewa; akwai Cibiyar Lafiya ta Tarayya da aka ware domin Suleja, amma aka karkatar da ita zuwa wani gari a cikin jihar.

Yankin Masarautar Suleja, shi ne mafi tasiri a fannin tattalin arziki a Jihar Neja, saboda kusancinsa da babban birnin tarayya. Gwamnatin Jihar Neja, na ci gaba da cin moriyar hakan ta hanyar tara haraji masu tarin yawa kamar PAYE, kudin filaye da kadarori da sauran haraji. Masarautar Suleja ita kadai na ba da akalla kashi 40 cikin 100 na kudaden da jihar ke samu daga cikin gida. Kudaden harajin da ake tarawa daga Karamar Hukumar Suleja, sun fi na kowace karamar hukuma a jihar. A kwana-kwanan nan, gwamnan ya bayyana haka.

Amma fa, idan aka kwatanta da wasu garuruwa a cikin jihar, ingancin titin da ake ginawa a cikin birnin Suleja, bai kai kima ba ko kadan. Daga Maje zuwa Madalla, ana iya cewa kwangila ce ta biliyoyin Nairori. Amma kuma, babu wani allon kwangila da ke bayyana sunan dan kwangilar ko hukumar da ke sa ido. Wannan yana nuna irin gazawar da ake da ita wajen gaskiya da rikon amana cikin mulki.

Jama’ar Suleja da masu kaunar garin, ba su da wani zabin da ya wuce su saka a ransu cewa; wata boyayyar makarkashiya ce aka shirya, don rage kudin aikin domin amfanuwar wasu. Wannan kuwa, wata shaida ce ta yadda ake yi wa wanda ke kawo riba wulakanci. Abin takaici ne a ce garin da ke bayar da kudaden shiga ya zama wanda aka watsar da shi a fannin gine-gine da walwalar jama’a.

Za a ci gaba In Shaa Allah.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Suleja
ShareTweetSendShare
Previous Post

Ƴan Ta’adda 13,500 Aka Kashe Cikin Shekaru 2 – NSA Ribadu

Next Post

GORON JUMA’A

Related

Ranar Hausa: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka
Bakon Marubuci

Ranar Hausa: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

1 day ago
Yaushe Shugaban Kasa Zai Ba ‘Yan Matan Yobe Nasu Kyaututtukan
Bakon Marubuci

Yaushe Shugaban Kasa Zai Ba ‘Yan Matan Yobe Nasu Kyaututtukan

1 week ago
Hoton Kwankwaso da Ganduje da Shekarau
Bakon Marubuci

Daga Sawaba Zuwa Asara: Baje Kolin Kasuwancin Siyasa A Kano – Auwalu Anwar

2 weeks ago
Manufofin Hulda Da Kasashen Wajen Da Nijeriya Ke Bukata
Bakon Marubuci

Manufofin Hulda Da Kasashen Wajen Da Nijeriya Ke Bukata

2 weeks ago
Hadarin Da Ke Kunshe Da Jin Bangare Daya Na Labari
Bakon Marubuci

Hadarin Da Ke Kunshe Da Jin Bangare Daya Na Labari

2 months ago
Yawaitar Al’umma: Martanin Karl Marx Ga Rabaran Malthus
Bakon Marubuci

Yawaitar Al’umma: Martanin Karl Marx Ga Rabaran Malthus

2 months ago
Next Post
Goron Sallah

GORON JUMA'A

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Gana Da Narendra Modi 

Xi Jinping Ya Gana Da Narendra Modi 

August 31, 2025
Xi Jinping Da Uwargidansa Peng Liyuan Sun Shirya Liyafar Maraba Da Baki Na Kasa Da Kasa Ga Mahalarta Taron SCO

Xi Jinping Da Uwargidansa Peng Liyuan Sun Shirya Liyafar Maraba Da Baki Na Kasa Da Kasa Ga Mahalarta Taron SCO

August 31, 2025
Gobarar Tankar Mai Ta Lakume Manyan Motoci 4 A Legas

Gobarar Tankar Mai Ta Lakume Manyan Motoci 4 A Legas

August 31, 2025
Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Farfado Da Kasa Bisa Karfin Ruhin Turjiya Ga Zalunci

Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Farfado Da Kasa Bisa Karfin Ruhin Turjiya Ga Zalunci

August 31, 2025
Kano Na Asarar Biliyan 1 Duk Shekara Dalilin Rashin Yin Gwanjon Tsofaffin Kayan

Kano Na Asarar Biliyan 1 Duk Shekara Dalilin Rashin Yin Gwanjon Tsofaffin Kayan

August 31, 2025
Kasar Sin Ta Inganta Wuraren Tunawa Da Tarihi Don Bikin Samun Nasara Kan Zaluncin Japanawa

Kasar Sin Ta Inganta Wuraren Tunawa Da Tarihi Don Bikin Samun Nasara Kan Zaluncin Japanawa

August 31, 2025
Jami’an Senegal Sun Yaba Da Ci Gaban Da Aka Samu Wajen Aiwatar Da Sakamakon Taron FOCAC Na Beijing

Jami’an Senegal Sun Yaba Da Ci Gaban Da Aka Samu Wajen Aiwatar Da Sakamakon Taron FOCAC Na Beijing

August 31, 2025
Ɗan Majalisa Zai Saya Wa Makinde Fam Ɗin Takarar Shugaban Ƙasa A 2027

Ɗan Majalisa Zai Saya Wa Makinde Fam Ɗin Takarar Shugaban Ƙasa A 2027

August 31, 2025
Fim Din Kasar Sin Kan Kisan Kiyashin Nanjing Ya Ja Hankulan Masu Kallo A Nijeriya

Fim Din Kasar Sin Kan Kisan Kiyashin Nanjing Ya Ja Hankulan Masu Kallo A Nijeriya

August 31, 2025
Hatsarin Jirgin Kasa: Gwamna Uba Sani Ya Ba Da Umarnin Talllafawa Fasinjojin Da Ke Cikin Jirgin

Hatsarin Jirgi: Babu Batun Zagon-ƙasa Ga Harkokin Sufurin Jiragen Ƙasan Abuja-Kaduna – Gwamnati

August 31, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.