• English
  • Business News
Thursday, July 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ko Kwamitin Saraki Zai Iya Ceto PDP Daga Rikicin Cikin Gida?

by Yusuf Shuaibu
1 month ago
in Tambarin Dimokuradiyya
0
Ko Kwamitin Saraki Zai Iya Ceto PDP Daga Rikicin Cikin Gida?
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Yayin da zaben 2027 ke kara karatowa, babbar jam’iyyar adawa ta Nijeriya wato PDP, ta fada cikin rarrabuwan kai, radani da kuma sauya sheka daga wasu fusatattun ‘ya’yanta.

Bisa ci gaba da fuskantar sauya shekar mambobinta zuwa jam’iyyar APC mai mulki da kuma rikicin cikin gida, PDP ta fahimci cewa akwai bukatar daidaita lafiyarta kafin lokaci ya kure mata.

  • Masanan Najeriya Sun Bayyana Muhimmancin Hadin Gwiwar Afirka Da Sin A Fannin Tinkarar Kalubalen Harajin Kwastam Na Amurka
  • Yawan Wutar Lantarkin Da Sin Ke Iya Samar Ta Amfani Da Karfin Ruwa Ta Kai Matsayin Koli A Duniya

Don aiwatar da wannan muhimmin aiki, gwamnonin da tsofaffin gwamnonin da aka zaba karkashin jam’iyyar sun bukaci tsohon shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki ya jagoranci aikin ceto jam’iyyar daga rugujewa.

An dora wa tsohon gwamnan Jihar Kwara alhakin jagorantar tattaunawar zaman lafiya a tsakanin bangarorin PDP masu rabuwan kai da warware rikicin game da matsayin sakataren jam’iyyar kafin zaben 2027.

Aikin da aka dora wa Saraki yana da mutukar wahala, don haka masana harkokin siyasa ke ci gaba da saka alamar tambaya kan cewa zai iya kawo zaman lafiya a jam’iyyar PDP?

Labarai Masu Nasaba

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin Fadar Shugaban Kasa Da Peter Obi Kan Tallafin Mai

Sauya Sheka Ya Sa APC Ta Samu Gagarumin Rinjaye A Majalisun Tarayya

PDP na fama da rikicin cikin gida mafi muni a tarihin jam’iyyar. Tun lokacin da jam’iyyar ta rasa shugabanci a 2015, ta ci gaba da fuskantar matsaloli wajen magance rikicin da take fama da shi. Ko wani zabe yana zuwa da nashi kalubalan, yana bayyana cin amana na cikin jam’iyya.

Zaben 2023, jam’iyyar ta bai wa Atiku Abubakar takarar shugaban kasa, wanda shi dan Arewa ne, inda lamarin ya haifar da fushi na masu ruwa da tsaki daga kudancin kasar nan, musamman daga wajen ministan Abuja na yanzu, Nyesom Wike.

Haka ma a daidai lokacin da ake kara fuskantar zaben 2027, wannan yanayi na sake kara bayyana adaidai lokacin da Atiku ke kokarin samun tikitin jam’iyyar. A lokaci guda, Wike ya bayyana matsayinsa a fili kan zaben da ke tafe.

A wani taron manema labarai na kwanan nan, tsohon gwamnan Jihar Ribas ya yi gargadin kar jam’iyyar ta bai wa wani dan takarar shugaban kasa daga yankin Arewa, ya yi hasashen cewa PDP za ta sake shan kaye idan har ta kara yin wannan kuskuren.

Ko shugabannin PDP sun ji dadin hakan ko ba su ji dadin ba, matsayin Wike ya dace da mutanen Kudu, wadanda ke ganin yankinsu ya cancanta ya kammala shugabancin shekaru takwas kafin mulki ya dawo Arewacin Nijeriya.

Matsalar tsarin karba-karba ta kunno kai ne bayan da Atiku ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023, madadin kira na neman dan takara daga Kudu.

Wannan ya bai wa Wike damar yakar PDP. Lmarin da ya kulla dangantaka da APC, wanda ya sanya shi ya zama babban abokin hamayya a jam’iyyar.

Yanzu, PDP na fuskantar wannan yanayin na bin tsarin karba-karba kafin 2027. Masu nazarin harkokin siyasa na jiran ganin yadda za ta kaya a wannan lamari tsakanin Kudu da Arewa.

Duk da haka, yayin da masu ruwa da tsaki daga Arewa ke ganin cewa yawansu na iya taimaka wa PDP dawo da iko, abokansu daga Kudu sun yi imani da cewa fitar da dan takarar shugaban kasa daga yankinsu zai taimaka wa jam’iyyar wajen dawo da wurare masu mahimmanci da suka rasa.

Dangane da wannan, Saraki na jagorantar kwamitin sulhu da ke fuskantar kalubale masu yawan gaske. An da dora masa alhakkin dawo da martaban jam’iyyar da sulhunta tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar masu mukami da wadanda ba su da mukami.

An dai nada Saraki wannan matsayin ne saboda dabarunsa na tsare-tsare da iya yin sulhu, ya shawo kan manyan batutuwan siyasa a cikin tarihinsa. Haka ma ko a lokacin da ya zama shugaban majalisar dattawa ya samu nasarar hada kan ‘yan majalisa a cikin yanayi na muni wajen shugabanci.

Duk abin da Saraki ke shirin yi, matakan sulhunsa dole ne su hada da shirye-shiryen da za su gamsar da masu goyon bayan Wike, sake hada masu ruwa da tsaki daga kowane yanki da kuma sake fasalta rabon mukamai na jam’iyyar don kawo daidaiton siyasa a Nijeriya. Wannan aiki ne mai wahala, amma ‘yan Nijeriya da dama na ganin cewa Saraki yana da kwarewar siyasa da zai iya yin wannan jan aikin idan har jam’iyyar ta ba shi dama.

Idan har kokarin sulhu na Saraki ya gaza, to a bayyana yake PDP za ta rasa madafa, sannan za ta kara fadawa cikin Rashin tabbas. Amma idan ya yi nasara, zai iya dawo da martabar siyasar jam’iyyar a Nijeriya.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: PDPSaraki
ShareTweetSendShare
Previous Post

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Gwamnatin Jamus Friedrich Merz

Next Post

Kungiyar Tsofaffin ÆŠaliban BUK Ta Karrama Dr. Sani Dauda Ibrahim Da Walimar Kammala Digiri Na 3

Related

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin Fadar Shugaban Kasa Da Peter Obi Kan Tallafin Mai
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin Fadar Shugaban Kasa Da Peter Obi Kan Tallafin Mai

3 weeks ago
APC
Tambarin Dimokuradiyya

Sauya Sheka Ya Sa APC Ta Samu Gagarumin Rinjaye A Majalisun Tarayya

3 weeks ago
Adawa
Tambarin Dimokuradiyya

Yadda Rarrabuwar Kawunan Jam’iyyu Zai Iya Sauya Alkiblar Zaben 2027

4 weeks ago
‘Yancin Kananan Hukumomi: Shekara Daya Da Hukuncin Kotun Koli Amma Ba A Aiwatar Ba
Tambarin Dimokuradiyya

‘Yancin Kananan Hukumomi: Shekara Daya Da Hukuncin Kotun Koli Amma Ba A Aiwatar Ba

1 month ago
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya
Tambarin Dimokuradiyya

‘Yan Adawa Na Cacakar APC A Yankin Arewa Maso Yamma Bisa Goyon Bayan Tazarcen Tinubu

1 month ago
Shugaban INEC Ya Yi Kira Da A Sake Fasalin Tsarin Zabe Gabanin 2027
Tambarin Dimokuradiyya

Shugaban INEC Ya Yi Kira Da A Sake Fasalin Tsarin Zabe Gabanin 2027

2 months ago
Next Post
Kungiyar Tsofaffin ÆŠaliban BUK Ta Karrama Dr. Sani Dauda Ibrahim Da Walimar Kammala Digiri Na 3

Kungiyar Tsofaffin ÆŠaliban BUK Ta Karrama Dr. Sani Dauda Ibrahim Da Walimar Kammala Digiri Na 3

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 1,191, Sun Ceto 543 Cikin Watanni Uku

Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 1,191, Sun Ceto 543 Cikin Watanni Uku

July 3, 2025
Sin Ta Bai Wa Habasha Kayayyakin Tallafin Jinya

Sin Ta Bai Wa Habasha Kayayyakin Tallafin Jinya

July 3, 2025
Dutsen Da Amurka Ta Jefa Ya Fado Kasa

Dutsen Da Amurka Ta Jefa Ya Fado Kasa

July 3, 2025
Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 50 A Benue

Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 50 A Benue

July 3, 2025
Gwamnatin Yobe Ta Rufe Kasuwanni Uku Saboda Fargabar Hare-haren Boko Haram

Gwamnatin Yobe Ta Rufe Kasuwanni Uku Saboda Fargabar Hare-haren Boko Haram

July 3, 2025
ÆŠan Wasan Liverpool, Diogo Jota, Ya Mutu A Hatsarin Mota

ÆŠan Wasan Liverpool, Diogo Jota, Ya Mutu A Hatsarin Mota

July 3, 2025
Mun Shirya Fuskantar APC Domin Ceto Talakawa – Abubakar Malami

Mun Shirya Fuskantar APC Domin Ceto Talakawa – Abubakar Malami

July 3, 2025
An Yi Wa ‘Yar Shekara 18 Fyade Har Lahira A Taraba

’Yansanda Sun Ceto Ɗan Ghana, Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 3

July 3, 2025
Buhari Ba Shi Da Lafiya, Amma Yana Samun Sauƙi A Birtaniya — Garba Shehu

Buhari Ba Shi Da Lafiya, Amma Yana Samun Sauƙi A Birtaniya — Garba Shehu

July 3, 2025
Kayayyakin Sin Sun Kara Baiwa Masu Sayayya Na Kasa Da Kasa Damar Samun Zabi

Kayayyakin Sin Sun Kara Baiwa Masu Sayayya Na Kasa Da Kasa Damar Samun Zabi

July 2, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.