Shugaban Kamfanin Man Fetur na kasa NNPCL, Bayo Ojulari, ya sanar da shirye-shiryen dawo da ayyukan ci gaba da neman Man a Kolmani, da ke a yankin Arewa maso Gas.
Idan za a iya tunawa, a ranar 22 na watan Nuwambar 2022 ne, tsohuwar Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta kaddamar da aikin hako Man na Kolmani, wanda aikin ya kasance, shi ne na farko da aka fara gudnarwa a Arewacin kasar.
- ‘Yan Adawa Na Cacakar APC A Yankin Arewa Maso Yamma Bisa Goyon Bayan Tazarcen Tinubu
- Gamayyar kungiyoyin Seyi Tinubu (STSG) Na Shirin Gangamin Taronta Na Kasa
Ojulari wanda ya sanar da hakan a hirarsa da kafar BBC a ranar Litinin ya yi kira ga alumomin da ke a yankin na Arewa maso Gabas da su kawantar da hankulansu tare da ba su tabbacin cewa, za a sake dawo da aikin na neman Man a Kolmani da ke a yankin Arewa maso Gabas.
“Zamu dawo da aikin na neman Man a Kolmani da kuma a sauran guraren da ake hasashen akwai Man Fetur din, baya ga batun neman Man, mun kuma mayar da hankali wajen kammala aikin sanya Bututun Danye daga Ajaokuta zuwa jihar Kano,” Inji Ojulari.
Ya sanar da cewa, wadannan ayyukan, za su taimaka wajen sake dawo da masana’antu da durkushe da kuma sake kafa wasu sabbin masana’antu.
“Wannan ci gaban zai kuma taimaka wajen kara habaka tattalin ardikin da ke a yankin na Arewa maso Gabas, wanda hakan ya zame mana wajbi, mu sake dawo wajen yin aikin domin aikin ya ci gaba da tafiya,” A cewar Ojulari.
Kan batun rikicin da yaki ci, yaki cinyewa a tsakanin Kamfanin na NNPCL da kuma rukunomin Kamfanin Dangote Ojulari ya bayyana cewa, ana ci gaba da kokari domin a kawo karshen rikicin.
“Dangote ya bayar da gagarumar gudunmawa wanda kuma, ya cannaci a yaba masa, za mu kuma yi hadaka domin mu tabbatar da, mun ci gaba da samar da wadataccen Man Fetur ga ‘yan kasar nan,” Inji Sabon Shugaban.
“Ana samun masalaha kan komai ne, ta hanyar tattaunawa za mu yi aiki kafada da kafada, domin amfanin ‘yan Nijeriya,” A cewar Ojulari.
Kazalika, da yake yin tsokaci kan batun samun raguwar farashin Danyen Mai a kasuwar duniya wanda hakan ya sanya burin samun kudaden shiga na kasar ya ragu, ya sanar da cewa, hakan ya shafi kasafin kudin kasar, duba da cewa, akasarin hasashen kasar ya dogara ne, kan samun kudin shiga na Man.
Ya sanar da cewa, NNPCL na kan aikin rage kashe kudaden gudanar da ayyukansa, wanda hakan zai bai wa Kamfanin damar yin amfani da kudaden shigar da yake samu, ta hanyar sayar da Man Fetur da na Iskar Gas.
Kan korafin da wasu yan kasar ke yi, kan rashin raguwar farashin Man Fetur da ake sayarwa a kasar, duk da cewa, farashinsa ya ragu a kasuwar duniya ya ce, Dilolin Man na bukatar lokaci, domin rage farashinsa.
“Idan Dilalan sun sayi Man kafin farashinsa ya ragu, suna bukatar su sayar da shi ne, kan tsohon farashi, amma idan sun saye shi kasa da sabon farashi, muna sa ran farashin ya sauka wanda zai nuna cewa, an samu sauyi,” Inji Ojulari.
A cewar NNPCL, tarin aikin na neman Man na Kolmani, an faro shi ne, tare da Kamfanin Mai na Shell a 1970, amma daga baya, aka yi watsi da aikin domin ba samu wata gagarumar cimma nasara ba.
Sai dai, daga baya an sake dawo da aikin ta hanyar Kolmani Riber 2, 3, and 4 a shekarar 2019, wanda hakan ya sanya aka gano Gangunan Danyen Mai biliyan daya da kuma Iskar Gas biliyan 500.
NNPC a ya sanar da cewa, a 2019 ya sake gabata da bukatar a yi amfani da kimiyyar zamani domin a ci gaba da aikin na nemna Man Kolmani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp