Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai wa ayarin motocin uwargidan Gwamnan Jihar Osun, Misis Kafayat Oyetola, hari da yammacin ranar Juma’a.
Duk da cewa har ya zuwa yanzu babu wani bayani kan lamarin, majiya daga garin Owode, Ede, inda lamarin ya faru, ta ce ayarin motocin Misis Oyetola na kan hanyar zuwa Osogbo kuma suna kusa da kasuwar Owode ne aka ji karar harbe-harbe da misalin karfe 8 da daren ranar Juma’a.
- Dakarun Sojoji Sun Dakile Shirin Garkuwa Da Mutane, Sun Ceto Mutane 3 A Kaduna
- Kananan Sana’oi Da Ci Gaban Kasa (4)
Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa da Alayande, ya shaida wa wakilinmu yau Asabar cewa wata babbar mota ce ta kawo cikas ga cunkoson ababen hawa a lokacin da ayarin motocin suka isa mahadar kasuwar Owode.
“A lokacin da ake kokarin sa direban babbar motar ya matsa ne aka samu sabani tsakanin jami’an tsaro da ke tare da ayarin motocin.
“Na ji karar harbe-harbe da dama inda na tsaya kusa da mahadar. Ga shi duhu ne amma an samu sabani tsakanin jami’an tsaro da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne,” inji shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Osun, Yemisi Opalola, ba ta mayar da martani ga sakon da aka aike mata kan lamarin ba.
Sai dai jami’in yada labarai na ofishin uwargidan gwamnan, Oluwatunmise Iluyomade, ta tabbatar da kai wa ayarin motocin hari.
Ta ce “Ba a samu asarar rai ba a harin. Sai dai waasu jami’an tsaro da ke tare da ayarin motocin sun samu raunuka.”