Al’ummar Jihar Yobe sun na ci gaba da alhinin kisan gillar da aka yi wa Shehin Malamin addinin Musulunci, Sheikh Goni Aisami Gashuwa, wanda ake zargin wasu jami’an tsaro ne suka kashe shi.
Ana zargin sun kashe shi da misalin karfe 10:00 na daren ranar Juma’a, kan hanyarsa ta dawowa daga Kano zuwa Gashuwa.
- Yanzu-Yanzu: SSANU Da NASU Sun Janye Yajin Aiki Bayan Ganawa Da Ministan Ilimi
- Babu Wanda Zai Fice Daga NNPP Da Zai Girgiza Siyasar Kwankwaso – Kofa
Kamar yadda wata majiya daga bakin wani jami’in tsaro a garin Jaji-maji, shelkwatar karamar hukumar Karasuwa ya shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa, maharan sun biyo shi ne a mota kirar Sharon, wanda suka tare motarsa bayan ya fita daga kauyen Chakama mai tazarar kilomita 3 zuwa garin Jaji-maji.
“Shi kadai ne a motar kuma da alama sun biyo shi ne ne bisa zaton yana dauke da kudi, a kan hanyarsa daga Kano zuwa gida. Wanda bayan sun harbe shi a ciki tare da soka masa wuka a jiki, sannan suka ja gawarsa zuwa gindin kaba. Kuma cikin ikon Allah basu bar inda gawarsa take ba har gari ya waye.”
“Ana haka sai ga jama’a masu tafiya gona, wanda nan take suka shaida wa Lawanin Jaji-maji, Lawan Manaja inda nan take ya nemi ‘yansanda da ke aiki a garin.” In ji majiyar.
Bugu da kari, majiyar tsaro a garin Jaji-maji ta bayyana cewa, “Ana zargin wasu sojoji biyu da kisan malamin, wanda kuma tuni ‘yansanda suka kama su tare da bindigogi biyu.
“Sannan zancen da nake da kai yanzu haka an garzaya dasu zuwa Damaturu, babban birnin Jihar Yobe don ci gaba da bincike,” a cewarsa.
A hannu guda kuma, wannan rashi na Sheikh Goni Aisami Gashuwa, ya tayar da hankulan al’ummar garin Gashuwa da Jihar Yobe baki daya, saboda kasancewarsa mutum mai kokari kuma Malami mai karantar da al’umma sama da shekaru 30 da suka gabata.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan Jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar wa da wakilinmu a jihar cewa, sun samu bayanin afkuwar lamarin tare da kokarin da jami’ansu a garin suka yi na kama wadanda ake zargi da aikata laifi.
Ya kara da cewa yanzu haka suka hannun jami’an tsaron binciken manyan laifuka (CID) a Damaturu.