ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kocin Inter Milan Simone Inzaghi Ya Bar Kungiyar Kwanaki Biyu Bayan Rashin Nasara A Hannun PSG

by Rabilu Sanusi Bena and Sulaiman
7 months ago
Inzaghi

Inter Milan da kocinta Simone Inzaghi sun raba gari ta hanyar yarjejeniya, kwanaki uku bayan da Paris St-Germain (PSG) ta doke su a gasar cin kofin zakarun Turai. Inzaghi mai shekaru 49, wanda kulob din Serie A din ya nada a shekarar 2021, yana da alaka mai karfi tsakaninshi da kungiyar Al-Hilal ta kasar Saudiyya.

“Lokaci ya yi da zan yi bankwana da wannan kulob bayan aikin shekaru hudu, inda na ba da komai domin samun nasararta,” in ji Inzaghi wanda ya lashe kofuna shida a Inter.

ADVERTISEMENT
  • ‘Yansanda A Kano Sun Gargaɗi Sarki Sanusi II Kan Fitowa Hawan Sallah
  • Yanzu-yanzu: JUSUN Ta Dakatar Da Yajin Aikin Da Fara A Faɗin Ƙasa Baki Ɗaya

“Ina so in furta kalma daya ta karshe ga miliyoyin magoya bayan Nerazzurri (Inter) wadanda suka taya ni murna a lokacin nasara, hakazalika suka taya ni kuka a lokuta masu wahala kuma suka yi dariya da murna a kofuna shida da muka samu tare”.

LABARAI MASU NASABA

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Sanarwar tafiyar tasa ta biyo bayan ganawar da Inzaghi ya yi da jami’an Inter a ranar Talata, sanarwar da Inter Milan ta fitar ta ce Kulob din da Simone Inzaghi sun yanke shawarar rabuwa, “Wannan shi ne shawarar da aka dauka bisa yarjejeniyar juna”, shugaban Inter Giuseppe Marotta ya kara da cewa “Ina so in gode wa Simone Inzaghi saboda aikin da ya yi, ya matukar taka rawar gani a shekaru 4 da muka shafe muna aiki tare, don haka Inter Milan na yi mashi fatan alheri a duk inda zai samu kanshi a nan gaba”.

Inzaghi ya lashe gasar Seria A daya, Coppa Italia biyu da kuma Supercoppa Italia sau uku a lokacin da ya ke San Siro, sau biyu ya jagoranci Inter zuwa wasan karshe na gasar zakarun Turai amma Manchester City ta doke su da ci 1-0 a 2022-23 sannan suka sha kashi a hannun PSG da ci 5-0 a ranar Asabar din da ta gabata.

Sun kuma kasa cin kofin Seria A na 2024-25 bayan da Napoli ta basu maki daya kacal akan teburi, tafiyar Inzaghi na zuwa ne gabanin halartar Inter a gasar cin kofin duniya na kungiyoyin kwallon kafa na Fifa da aka fadada, wanda zai gudana a Amurka tsakanin 14 ga watan Yuni zuwa 13 ga Yuli.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal
Wasanni

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco
Wasanni

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey
Wasanni

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Next Post
Manufar Bude Kofa Ta Shaida Niyyar Sin Ta Ingiza Dunkulewar Duniya

Manufar Bude Kofa Ta Shaida Niyyar Sin Ta Ingiza Dunkulewar Duniya

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.