Tsohon Kakakin Majalisar wakilai ta tarayya, Rt. Hon. Yakubu Dogara ya aike da wasikar korafi wa Sufeto Janar na ‘yansandan Nijeriya, IGP Usman Baba Alkali dangane da zargin yunkurin kasheshi da wani dan mazabarsa ke yi.
Tsohon Kakakin ya bayyana sunansa wanda ke kokarin kashe sa din da cewa shine Barau Joel Amos wanda a cewarsa balo-balo ya yi ikirarin zai sayi bindiga tare da kashe shi da wasu ‘yan mazabarsa su uku masu suna Barr. Istifanus Bala Gambar, Rabaran Markus Musa (Shugaban kungiyar Kiristoci na Tafawa Balewa) da Mr. Emmanuel (Shugaban NL, na T/Balewa).
Yakubu Dogara ya shaida wa IGP Alkali cewa akwai zargin hada kai da wasu jami’an ‘yansanda masu suna Insifekta Dakat Samuel da Insifekta Auwalu Mohammed da shi Barau Joel Amos (Sarkin Yaki) wajen shirya wannan makarkashiyar tare da sayen bindigogi a hannunsu domin kashe shi.
Dogara ya shaida wa shugaban ‘yansandan cewa tunin kes din yake gaban DCP na sashin binciken na manyan laifuka ta rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, amma bisa girman lamarin ya ga dacewar sanar da shi domin fadada bincike, “Batu ne da ya shafi sace makamanku daga wasu jami’an da aka daura wa alhakin kula da makamai a wurin adanasu, shi Barau Joel Amos ko zai saya ko yana ma yana sayen bindigogi daga wajen jami’an.”
Dogara ya kara da cewa abun mamakin shine babu wani shawara a hukumance da ‘yansanda suka fitar dangane da wannan mummunar barazanar da ake yi wa rayuwarsu duk kuwa da cewa ana samun kesa-kesan garkuwa da mutane da kashe wasu ma musamman a gundumar Lere da ke karamar hukumar Tafawa Balewa a jihar Bauchi.
Dogaran sai ya buga misali da harin baya-bayan nan da wasu ‘yan bindiga suka kai kauyen Boto da ke gundumar Lere inda suka yi garkuwa da ‘yan uwan tsohon gwamnan Jihar Bauchi, Ahmadu Adamu Mu’azu da kashe wani, kan hakan ya nuna cewa akwai bukatar daukan matakan kan lamarin.
Ya ce irin wannan lamarin abun ne da ke bukatar gaggauta daukar matakin tare da cafke Barau Joel Amos domin zufafa bincike.
Hon. Yakubu Dogara ya kuma ce akwai matukar bukatar a binciki Barau Amos kan matsalolin tsaro da suke faruwa a yankin tare da bincikar inda yake samun kudaden sayen makamai tare da bibiyar bayanan shigar kudi da fitar kudi na asusun ajiyarsa hadi da binciken wayarsa.
Ya ce akwai bayanan da suke da su da dama da ke nuna cewa shi Barau Joel Amos na da hannu a zarge-zarge da dama don haka akwai bukatar a tsare shi tare da zurfafa bincike a kansa.
Ya yi fatan cewa Shugaban na ‘yansanda ba zai yi wasa da wannan batun ba inda zai kaddamar da bincike domin tabbatar da inganci tsaro da kare rayuka da dukiyar jama’an yankin.