Wani rahoto na gungun kwararru da aka fitar a Lahadin nan, ya nuna yadda kasar Sin ke ta kokarin samar da kyakkyawan yanayin zaman lafiya, da kawance, da hadin gwiwa a yankunan tekun kudancin kasar.
Rahoton na kwararrun cibiyar Xinhua, mai alaka da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin wato Xinhua, na da lakabin “Mayar da tekun kudancin Sin wuri mai cike da zaman lafiya, kawance da hadin gwiwa: matakan da Sin ke dauka”, ya ce har kullum Sin na nacewa matakan wanzar da zaman lafiya, da daidaito a yankunan tekun kudancin kasar, kuma nasarar hakan na da alaka da matakan hadin gwiwa da ake aiwatarwa tsakanin Sin da kasashe mambobin kungiyar ASEAN.
Rahoton ya kara da cewa, ta hanyar zurfafa amincewa da juna, da hadin gwiwa mai game da dukkanin sassan siyasa, da tattalin arziki, da al’adu, wannan hadaka ta samar da wani yanayi na cimma moriya mai dorewa ta bai daya. Sakamakon hakan, Sin ta zamo karfi abun dogaro dake wanzar da zaman lafiya da daidaito a shiyyarta, yayin da take ta ingiza hadin gwiwa da ci gaban yankin tekun kudancin kasar.
Har ila yau, Sin ta yi aiki tukuru wajen gina zaman lafiyar shiyya, ta hanyar amincewa da juna ta fuskar siyasa, da bunkasa cin moriyar tattalin arziki na bai daya, domin tabbatar da walwala a shiyyarta, da inganta dinkewar al’ummu, ta yadda za a cimma makomar bai daya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp