• English
  • Business News
Saturday, June 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Cikin Shekaru 2, Tinubu Ya Karɓo Bashi Fiye da Shugabannin Nijeriya 3 – Obi

by Abubakar Sulaiman
1 day ago
in Manyan Labarai
0
Cikin Shekaru 2, Tinubu Ya Karɓo Bashi Fiye da Shugabannin Nijeriya 3 – Obi
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya komar da dimokuraɗiyya baya, inda ya bayyana cewa tsarin mulki ya samu koma baya tun lokacin da ya hau mulki shekaru biyu da suka wuce.

Obi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fito a ranar Alhamis mai taken ‘Democracy in Decline: Reflecting on Two Years of Tinubu’s Governance’. Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce bayan nazari mai zurfi a kan shekaru biyu na mulkin Tinubu, babu shakka cewa gwamnatin ta kasa gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

  • Kashinku Ya Bushe: Sojoji Sun Lashi Takobin Kawo Ƙarshen ‘Yan Ta’adda A Zamfara Da Katsina 
  • Cikakken Jerin Sunaye: Tinubu Ya Karrama ‘Yan Nijeriya 102 Don Bukin Ranar Dimokuradiyya Ta 2025

Ya kuma koka cewa gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Tinubu ta kasa cimma burin cigaba a fannonin tattalin arziki, da tsaro, da yaki da cin hanci da rashawa, da kuma harkokin siyasa. Ya buƙaci shugaban ƙasar ya daina yawo ƙasashen waje, ya mayar da hankali kan ziyartar jihohin Nijeriya guda 36 a cikin sauran shekaru biyu na mulkinsa.

Dangane da taɓarɓarewar dimokuraɗiyya, Obi ya gargaɗi Tinubu da ya yi koyi da marigayi Shugaba Umaru Yar’Adua, wanda ya amince da cewa zaben da ya kawo shi mulki ba shi da inganci. Ya kuma nuna cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya ceci dimokuraɗiyya ta hanyar amincewa da kayen da ya sha a zaben 2015.

Obi ya ƙara da cewa, a halin yanzu, Nijeriya ba ta cikin tsarin dimokuraɗiyya na gaskiya, inda aka samu koma baya a fannonin tattalin arziki, da ilimi, da lafiya, da tsaron jama’a. Ya bayyana cewa kuɗin da aka karɓa a matsayin bashi bai yi tasiri ba, yayin da yawan talauci, da ficewar kamfanoni masu zaman kansu daga Nijeriya, da rashin abinci mai gina jiki ke ƙaruwar.

Labarai Masu Nasaba

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnati Ta Janye Taron Addu’ar Neman Wadatar Abinci

Majalisar Tarayya Na Ƙoƙarin Zama Ƴar Amshin Shata – Saraki

Ya kammala da cewa, “Gwamnatin ta yi amfani da kuɗaɗe da yawa fiye da gwamnatocin Yar’Adua, Jonathan, da Buhari jimilla, amma babu wani cigaba da aka samu.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Peter ObiTinubu
ShareTweetSendShare
Previous Post

Darussan Hadisin Aikin Hajjin Manzon Allah S.A.W (2)

Next Post

Bukatar Kara Yawan Masu Fitowa Kada Kuri’a A Zabuka Nan Gaba

Related

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnati Ta Janye Taron Addu’ar Neman Wadatar Abinci
Manyan Labarai

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnati Ta Janye Taron Addu’ar Neman Wadatar Abinci

7 hours ago
Majalisar Tarayya Na Ƙoƙarin Zama Ƴar Amshin Shata – Saraki
Manyan Labarai

Majalisar Tarayya Na Ƙoƙarin Zama Ƴar Amshin Shata – Saraki

1 day ago
nijeriya
Manyan Labarai

Yadda Badakalar Tallafin Man Fetur Ta Zame Wa Nijeriya Alakakai

1 day ago
Ba Zan Bar Nijeriya Ta Zama Kasa Mai Jam’iyya Daya Ba – Tinubu
Manyan Labarai

Ba Zan Bar Nijeriya Ta Zama Kasa Mai Jam’iyya Daya Ba – Tinubu

2 days ago
Sojoji Sun Kashe Auta, Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda Da Wasu 13 a Jihar Zamfara
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe Auta, Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda Da Wasu 13 a Jihar Zamfara

2 days ago
Zamfara: APC Za Ta Maka PDP A Kotu Kan Zargin Matawalle Da Hannu A Satar Mutane
Manyan Labarai

Zamfara: APC Za Ta Maka PDP A Kotu Kan Zargin Matawalle Da Hannu A Satar Mutane

2 days ago
Next Post
Bukatar Kara Yawan Masu Fitowa Kada Kuri’a A Zabuka Nan Gaba

Bukatar Kara Yawan Masu Fitowa Kada Kuri’a A Zabuka Nan Gaba

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Harba Tauraron Dan Adam Na Lura Da Yanayin Bala’u

Sin Ta Harba Tauraron Dan Adam Na Lura Da Yanayin Bala’u

June 14, 2025
An Samu Babban Canji Kan Tsarin Ciniki A Tsakanin Sin Da Afirka

An Samu Babban Canji Kan Tsarin Ciniki A Tsakanin Sin Da Afirka

June 14, 2025
Muhimmanci, Tasiri Da Kuma Amfanin Jigida Ga Mata

Muhimmanci, Tasiri Da Kuma Amfanin Jigida Ga Mata

June 14, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Isra’ila Da Ta Dakatar Da Kaddamar Da Hare-hare Kan Iran

Sin Ta Yi Kira Ga Isra’ila Da Ta Dakatar Da Kaddamar Da Hare-hare Kan Iran

June 14, 2025
Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Kara Habaka Daga Manyan Tsare-Tsare Zuwa Matakai Na Ainihi

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Kara Habaka Daga Manyan Tsare-Tsare Zuwa Matakai Na Ainihi

June 14, 2025
Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (1)

Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (1)

June 14, 2025
Wasu Abubuwa Da Ke Sa Maza Hana Mata Fita Unguwa (Uwargida)

Kula Da Kanki Bayan Haihuwa Abu Ne Muhimmi

June 14, 2025
Gwamnati Ta Yi Barazanar Matakai Masu Tsauri Kan Masu Fasa Bututun Mai

Gwamnati Ta Yi Barazanar Matakai Masu Tsauri Kan Masu Fasa Bututun Mai

June 14, 2025
Amfanin ‘Ya’yan Gwanda Da Yadda Ake Sarrafa Su

Amfanin ‘Ya’yan Gwanda Da Yadda Ake Sarrafa Su

June 14, 2025
DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnati Ta Janye Taron Addu’ar Neman Wadatar Abinci

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnati Ta Janye Taron Addu’ar Neman Wadatar Abinci

June 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.